✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birrai sun yi dabdala a tsakiyar birni a Thailand

Birrai a birnin Lopburi na kasar Thailand sun sha lagwada tare da dabdala a ranar Lahadin da ta gabata a wajen bikin Dabdala ta Birrai…

Birrai a birnin Lopburi na kasar Thailand sun sha lagwada tare da dabdala a ranar Lahadin da ta gabata a wajen bikin Dabdala ta Birrai ta Shekara da ake shiryawa a tsakiyar Thailand.

Kafar labarai ta AP, ta ce, a daidai lokacin da ake fama da cinkoson safiya, sai mutanen da suka yi shigar batum-batumi a matsayin birrai suka jejjeru a wajen wani tsohon ginin tarihi da ake kira Ancient Three Pagodas, yayin da ’yan sa-kai suka tsara abinci a gefen hanya domin birrai na gaskiya — a matsayin wani biki na yankin Lopburi mai nisan kilomita 150 a Arewa da birnin Bangkok.

Dimbin birrai sun keto a guje suka rika fada da juna suna warwason abincin da aka shirya masu, yayin da maziyarta da mutanen yankin ke ci gaba da tururuwar zuwa wajen.

An kai nau’o’in abincin da aka tsara zuwa wajen wani bautar gargajiya ne kafin birran su auka musu, wadanda galibi kayan marmari da aka ajiye su kashi-kashi.

Yayin da birran ke ci gaba da dabdala, sai masu shirya bikin suka nuna bikin fa ba na birrai kadai ba ne, suka shiga aka rika damawa da su.

“Wannan dabdala ta birrai ta samu nasara, kuma hakan yana kara taimakawa wajen bunkasa harkar yawon bude-ido a Lopburi a tsakanin kasashen duniya duk shekara,” in ji Yongyuth Kitwatanusont, wanda ya kirkiro bikin.

Ya ce, “A baya akwai kimanin birrai 300 a Lopburi kafin su karu zuwa kusan 4,000 daga baya.

“An san Lopburi da sunan birnin birrai, wanda ke nufin mutane da birrai suna iya rayuwa cikin jin dadi da lumana.”

Za a iya ganin haka ta yadda wasu birran suke hawa kan maziyarta ba tare da tsoro ba, haka sukan hau kan motoci da tebura.

A wasu lokuta birran sukan bar dimibin abincin da aka tanada masu su rika yin wasu abubuwan da suke sha’awa.

“Akwai wani biri da ya hau gadon bayana, a daidai lokacin da nake shirin daukar hoton kaina da waya. Ya wafci tabarau din da ke idona ya ruga ya hau turken wutar kan hanya yana kokarin ya cinye shi,” in ji Ayisha Bhatt, wata malamar Ingilishi ’yar Kalifoniya da take aiki a Thailand.

Sai dai masu kallo sukan yi taka-tsantsan kada birran su sace masu kaya.

“Mukan kula da su, maimakon barin su ga birran. Rashin yin nesa da su ya fi,” in ji Carlos Rodway, wani dan yawon bude-ido daga garin Cadiz na kasar Spain, wanda ya ce a baya wani biri ya dauke masa wani abu ya haye sama.

Bikin na bana mai taken “Birrai na ciyar da birrai” ana shirya shi ne a Lopburi fadar yankin don nuna jin dadi kan yadda birrai suke jawo masu yawon bude-ido.