✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya ta amince Chelsea ta sayar da tikitin kallon wasanni

Chelsea ta samu damar sayar da tikitin kallon wasan da za ta yi a gida da Real Madrid a Champions League.

Gwamnatin Birtaniya ta amince Chelsea ta sayar da tikitin kallon wasannin da za ta yi a waje da kuma wanda kungiyarta ta mata za ta fafata.

Tun farko gwamnatin Burtaniya ce ta yi gyara kan yadda za a gudanar da Chelsea, ciki har da hana sayar da tikitin allon wasanninta.

An hana Chelsea yin hada-hada tun bayan da gwamnati ta sa wa mai kungiyar, Roman Abromovich takunkumi, don mayar da martani kan harin da Rasha ke kai wa Ukraine.

Sai dai sauye-sauyen ya nuna cewa magoyan bayan Chelsea ba za su iya sayen tikitin kallon wasannin gida ba, amma ya saukaka wasu rashin tabbas da kungiyar da magoya bayanta ke fuskanta a yanzu.

A sabon tsarin da aka kaddamar duk kudin da aka samu kan sayar da tikitin zai shiga asusun Firimiyar Ingila, daga nan a raba ga masu hakki.

Kamar yadda aka yi sauyin lasisin kungiyar, kamfanin Roman Abromovic, Fordstam Ltd zai bayar da fam miliyan 30 kudin gudanar da Chelsea.

Haka kuma wannan tsarin zai bai wa Chelsea damar sayar da tikitin kallon wasan da za ta yi a gida da Real Madrid a Champions League ranar 6 ga watan Afirilu.

Haka kuma da karawar daf da karshe a FA Cup da za ta fafata da Crystal Palace a Wembley ranar 16 ga watan Afirilu.

Sashen wasanni na BBC ya ruwaito cewa, magoya baya daga waje za su iya sayen tikitin kallon Firimiyar Ingila a Stamford Bridge, inda kudin zai je asusun Firimiyar kai tsaye.

Haka kuma kungiyar Chelsea ta mata za ta buga gasar League da Reading ranar 3 ga watan Afirilu a Kingsmeadow.