Biyafara: Gwamnonin Kudu maso Gabas sun nesanta kansu da ’yan IPOB | Aminiya

Biyafara: Gwamnonin Kudu maso Gabas sun nesanta kansu da ’yan IPOB

    Sani Ibrahim Paki

Gwamnonin Jihohin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun nesanta kansu daga masu fafutukar ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biyafara.

Sun kuma yi Allah-wadai da hare-haren da suka biyo bayan fafutukar, wadanda suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.

Idan dai za a iya tunawa, haramtacciyar kungiyar nan ta ’yan awaren Biyafara ta IPOB ta jima tana kokarin ganin yankin ya balle daga Najeriya.

To sai dai Gwamnonin sun yi wani taro a Enugu ranar Asabar domin tattauna matsalolin da suka addabi yankin da kuma hanyoyin lalubo bakin zaren.

Shugaban Gwamnonin, kuma Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi wanda ya yi magana a madadin takwarorin nasa ya ce, “Muna Allah-wadai kan dukkan abubuwan da masu fafutukar nan suke yi na tada-zaune-tsaye, ko a Kudu maso Gabas ko ma a kowanne yanki.

“Muna jaddada cewa mana tare da su, ba da yawunmu suke yi ba.

“Zargin da ake yi cewa jagororin wannan yankin sun yi gum da bakinsu a kan lamarin ba gaskiya ba ne.

“Mu ’yan kabilar Ibo, muna jaddada mubayi’armu ga Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya, wacce za a tabbatar da adalci, ’yanci, soyayya da kaunar juna a cikinta,” inji Gwamnonin.