✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biyayya ga Annabi ita ce sonsa na gaskiya

Bin Ma’aiki (SAW) ya zama wajibi a kan kowane Musulmi.

Godiya tabbata ga Allah Madaukakin Sarki. Salati da taslimi su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW).

Bayan haka, babu shakka ya ’yan uwa masu albarka, bin Ma’aiki (SAW) da biyayya gare shi cikin abin da muke so da abin da ba ma so, shi ne yake nuna mana muna kaunarsa.

Bin Ma’aiki (SAW) ya zama wajibi a kan kowane Musulmi.

Duk mai cewa, La’ila ha’illalah Muhammadur Rasulullah (SAW) ya zama tilas a gare shi, ya yi koyi kuma ya bi abin da Annabi Muhammad (SAW) ya yi masa umarni da bi, ko da ba ya son wannan abu.

Kuma ya hanu daga abin da Annabi Muhammad (SAW) ya hana shi ko da yana so.

Manzon Tsira (SAW), babu mai kyakkyawar dabi’a irinsa, Allah Ya tsarkake shi. Allah Yana cewa: “Lallai kana da kyawawan dabi’u masu girma.”

Allah Ya wanke kwakwalwarsa, Ya barrantar da shi daga hauka. Allah Ya wanke harshensa Ya barrantar da shi daga fadar son zuciyarsa. Ba batacce ba ne, kuma ba halakakke ba ne.

Babu son zuciya a tare da shi. Allah Ya ce duk abin da ya fito daga bakinsa, Allah ne Ya yi masa umarni. Ba ya hukunci da son zuciyarsa, duk abin da ya fada wahayi ne aka yi masa.

Wannan ya nuna cewa bin Ma’aiki (SAW) bai zama da baki kawai ba, ko da mutum ya shekara yana cewa ina son Ma’aiki (SAW), ko mutum ya shekara yana kida da waka da rawa, wannan bai nuna cewa hakika yana son Manzon Allah (SAW) ba.

Abin yake daidai wajen nuna soyayya ga Annabi (SAW) a ga kana yin abin da ya ce a yi, ko a ga ka bar abin da ya ce a bari kawai.

Ma’aiki (SAW) ya ce kada ka ci naman dan uwanka, kada ka yi fushi da dan uwanka, kada ka yi gaba da dan uwanka, kada ka binciko laifin dan uwanka. Idan aka same ka kana yin wadannan abubuwa za ka ce kanason Manzon Allah SAW?

Allah Ya ce: “Ka ce (musu): “Idan har kuna son Allah, to ku bi ni.” Ashe bin Ma’aiki (SAW) shi ne babban abin da ya wajaba a gare mu.

Ya ’yan uwa masu daraja! Allah Ya gwama sonSa da da’a a gare Shi da da’a ga Ma’aiki (SAW) a duk inda ka sani.

Hatta a Sallar nan, sai da Allah Ya gwama, a kiran Sallah sai da Allah Ya gwama, Ashe in akwai wani abu wanda za mu yi, don son Ma’aiki (SAW) shi ne yin abin da Allah Ya ce.

Manzon Allah (SAW) shi da kansa ya ce idan da abin da za ka yi masa wanda yana kabarinsa za a tayar da shi ya amsa, shi ne ka yi masa Salati.

Mafi karancin Salati shi ne ka ce Sallahu Alaihi Wasallam, wannan shi ne kake da garanti.

A ina ne aka ce ka zo ka yi rawa kuma Allah Ya ba ka lada? Ina ne aka ce ana yi maka kida kana rawa ya zama addini? Ina ne aka ce ka yi rawa Allah Ya ba ka lada?

Ga Sallah raka’a biyu da za ka yi ka samu ladan aikin Hajji da Umara. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk mutumin da ya yi Sallar Asuba a cikin jama’a kuma ya zauna a wurin da yake, har rana ta fito ya tashi ya yi Sallah raka’a biyu, (Manzon Allah SAW ya ce wanda ya yi haka), kamar ya yi aikin Hajji da Umara ne cikakku.”

Babu wata wahala ga Sallar Walaha duk ka bar wadannan ka je kana shan wahala, ya dan uwa bawan Allah ka yi tunani mana!

Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Lallai ku bi Allah Madaukaki sannan ku bi ManzonSa. Wadanda duk suka kauce wa Allah da ManzonSa, to Allah fa ba Ya kaunar kafirai.”

Sannan Allah Ya gargade mu a kan kada mu saba wa Manzon Allah (SAW) inda Yake cewa ahir din wadanda suke saba wa Manzon Allah (SAW), su ji tsoron wata masifa da za ta zo musu.

Masifar nan za ta iya zuwa ta kowace hanya. Kamar kullum mutum ya fita kasuwa babu ciniki, babu wanda zai zo ya sayi kayanka ita ma masifa ce.

Ko Allah Ya yi ta ba ka abubuwa ba ka godewa, ita ma masifa ce. Ko a hada maka kudi ka je Legas ko Fatakwal ko kasashen waje don ka sayo kaya, ka ce ’yan fashi sun kwace kudin alhalin ba haka ba ne, ita ma masifa ce. Hanyoyin masifa daban-daban, ga girgizar kasa ma masifa ce.

Haka kawai mutane su zo su same ku su yi ta kashewa da sunan addini, ita ma masifa ce. Kasuwanninmu su rika konewa ba dalili ma masifa ce.

Ya ’yan uwa masu daraja! Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Ba ya kamata ga mumini namiji ko mumina mace Allah Ya yanke hukunci ko Manzon Allah (SAW) ya yanke hukunci sannan (wannan mutum) ya ce zan yi tunani, ko zan duba in gani…”

Mumini ba ya yin haka. Allah Madaukakin Sarki Yana rantsuwa da ZatinSa cewa imaninsu bai cika ba, ba muminai ba ne har sai sun kawo abin da ya faru a tsakaninsu na kara gare ka ya Manzon Allah, sannan in ka yanke hukunci, su tafi suna murna da wannan hukunci babu wani da ya samu kunci a zuciyarsa.

Duk a Annabawa babu wanda Allah Ya yi wa wannan shaida sai Annabi (SAW).

Allah Yana cewa duk mutumin da ya yi fitona-fito da Ma’aiki (SAW) bayan gaskiya ta fito karara, to, abin da yake so za a ba shi.

In mulki kake nema ka saba wa Allah da Ma’aiki (SAW) watakila a ba ka mulkin, watakila kuma ba za a ba ka ba.

Idan dukiya kake nema watakila ka samu, watakila kuma ba za ka samu ba. Idan suna kake nema ka saba wa Allah da Ma’aiki (SAW) watakila ka samu sunan, watakila kuma ba za ka samu sunan ba.

Saboda haka Allah Yake cewa idan kuka yi sabani a tsakaninku, ni in ce wannan abin fari ne, kai ka ce wannan abin baki ne, to, a koma ga Allah.

Ma’aiki (SAW) Ya ce “Ina yi muku wasiyya da ku bi Allah kuma ku bi ManzonSa, ina yi muku wasiyya ku ji kuma ku bi ko da bawa ne za a sa ya shugabance ku.”

Ya ’yan uwa Musulmi! Allah Ya yi mana umarni mu bi Ma’aiki (SAW).

Halaka ita ce bin abin da ranmu yake so, saboda haka kirkiro abubuwa a danganta su ga addini zai kai mu ga hallaka.

Daga Hudubar Sheikh Muhammad Sulaiman Adam, Babban Limamin Masallacin Sultan Bello, Kaduna