✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Blanke za ta bar Bankin Raya Afirka

Mataimakiyar Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) Jennifer Blanke ta bayyana aniyarta na sauka daga kujerar. Sanarwar da Sashen Hulda da Jama’a na bankin ya…

Mataimakiyar Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) Jennifer Blanke ta bayyana aniyarta na sauka daga kujerar.

Sanarwar da Sashen Hulda da Jama’a na bankin ya fitar a ranar Laraba ta ce Blanke za ta ajiye aiki ne daga ranar 4 ga watan Yuli mai zuwa.

A wasikar bayyana aniyar barin aikiin nata, Blanke wadda ta fara aiki da AfDB a 2007 ta nuna godiya bisa dama da hadin kai da ta samu daga shugaban bankin Akinwumi Adesina.

A cewarta hakan ya ba ta damar bayar da muhimmiyar gudunmmuwa wurin kawo sauye-sauye da ci gaba masu ma’ana a bankin.