✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boka ya rataye kansa a Binuwai bayan abin duniya ya dame shi

Ya mutu ya bar mata uku da ’ya’ya hudu a duniya.

Wani Boka da duniya ta yi masa daurin dema a jihar Binuwai daga karshe dai ya yanke shawarar kashe kansa ta hanyar rataya.

Bokan, mai kimanin shekara 42 dai ya rataye kan nasa ne a gundumar Mbakuha da ke Karamar Hukumar Ushongo ta jihar ta Binuwai.

Mutumin, wanda aka bayyana sunansa da Terhemen Iorbee dai rahotanni sun ce an shafe kimanin sa’a 24 ana nemansa, kafin daga bisani a gano gawarsa tana reto a jikin wata bishiya a karshen mako.

Shaidu sun ce ko kafin faruwar lamarin, an ga Terhemen ya koma yin wasu bakin al’adu, lamarin da ya sa iyalansa suka fara shiga damuwa.

Ya mutu ya bar mata uku da ’ya’ya hudu a duniya.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin ta wayar salula.