✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Akwai ayar tambaya tsakanin gwamnati da sojoji – Dattawan Arewa

Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta ce gwamnatin tarayya da sojoji na da dimbin tambayoyin da su ke bukatar su amsa a kan yakin da su…

Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta ce gwamnatin tarayya da sojoji na da dimbin tambayoyin da su ke bukatar su amsa a kan yakin da su ke yi da ta’addanci a Najeriya.

Kungiyar na martani ne kan harin da aka sake kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a da ya yi sanadiyyar rasuwar wasu daga cikin masu tsaron lafiyarsa a kan hanyarsu ta zuwa Baga.

ACF a wata sanarwa da sakataren watsa labaranta, Emmanuel Yawe ya sanyawa hannu ranar Asabar ta ce harin ‘yan ta’addar na nuna yanke kaunar jama’a kan karfin jami’an tsaro na kare lafiya da dukiyoyin al’umma.

Ya ce, “Duk da tabbacin da mu ka sha samu daga sojoji da gwamnatin tarayya kan kyautatuwar harkokin tsaro da yaki da Boko Haram amma har yanzu hare-haren sun ki ci sun ki cinyewa.

“A harin da aka kai masa ranar Juma’a, rayukan jami’an ‘yan sanda takwas, sojoji uku da jami’an sakai guda hudu sun salwanta.

“Ko a makon da ya gabata, sai da aka kashe wani babban soja (Kanal Bako) ta hanyar kwanton bauna a garin Damboa na jihar ta Borno,” inji ACF.

Kungiyar ta ce ko a watan Yulin da ya gabata sai da aka kaiwa gwamnan hari lokacin da ya ke kai wata ziyarar aiki a jihar.

“Mu na kira ga jami’an tsaro da su kara azama wajen dawo da kwarin gwiwar da jama’a ke da shi, dole su kara himma,” inji su.

A cewar kungiyar, idan har za a iya kaiwa gwamna mai ci hari, to kusan hakan na alamta cewa babu wanda ya tsira a kasar.

Ta ce harin ya nuna akwai alamar tambaya wajen tabbatar tsaron lafiya da kuma komawar masu zama a sansanonin ‘yan gudun hijira kan yiwuwar komawarsu garuruwansu.