✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya

Gwamnan Borno ya sha da kyar a harin mayakan Boko Haram kan ayarin motocinsa

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya tsallake wani hari da ‘yan Boko haram suka kai masa a hanyarsa ta zuwa garuruwan Monguno da Baga domin raba kayan abinci ga ‘yan gudun hijira.

Mayakan sun kai kai harin ne bayan Zulum ya fito daga Baga, garin da ya shahara wajen sana’ar kifi kuma ‘yan Boko haram sun dade suna cin karensu ba babbaka a yanki.

Wani daga cikin jami’an tsaron da ke ayarin gwamna ya ce “Gwamna lafiyarsa kalau kuma babu wanda ya raunata. Motar da ke bayan ayarin gwamna ce aka kai wa hari kuma mun tarwatsa su. Gwamna yana cikin koshin lafiya”.

Aminiya ta ji cewar kafin Gwamna Zulum ya tafi Mungono ranar Litinin, akwai rade-radin cewar ‘yan Boko Haram sun kama wasu jami’an hukumar agajin gain jihar (SEMA), amma bai fasa tafiyar ba.

Shugaban hukumar, Yabani Kolo, ta tabbatar wa ‘yan jarida cewar an kai wa jami’anta hari amma ba ta yi cikakken bayani ba.

Bayan harin da aka kai masa a shekara 2019, wannan shi ne karo na biyu da gwamnan yake tsallake harin ‘yan Boko Haram jiharsa.