✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram na sansani a Jihar Nasarawa —Gwamna Sule

An cafke mutum 900 a samamen hadin gwiwar jami’an tsaro.

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya tabbatar da cewa ’yan tada kayar bayan Boko Haram sun shiga jihar.

Gwamna Sule ya yi wannan jawabi ne yayin da yake tattauna da manema labarai, a ranar Juma’a bayan ganawarsa da Shugaba Muhammad Buhari a Fadar Gwamnatin Tarayya.

Sule ya ce an samu ayyukan ta’addanci a jihar daga Darussalam, masu alaka da mayakan Boko Haram, sai dai yace an kama sama da 900, yayin samamen hadin gwiwar jami’an tsaro a jihar.

A cewarsa, wanda aka cafke din sun shaida wa jami’an tsaro alakarsu da Boko Haram, amma ya ce gwamnatin jihar za ta dauki matakin da ya ce, shi ya sa ma ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari kan lamarin.

Ya kara da cewa, ganawarsa da shugaba Buhari, sun yi ta kan matsalar tsaro da ta shafi jihar, tare da neman taimakon Gwamnatin Tarayya, kan yadda za a kawo wa jihar dauki.