✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Sojoji na neman mutum 81 ruwa a jallo

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kaddamar rukuni na hudu na mayakan Boko Haram 81 da take nema ruwa a jallo

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kaddamar rukuni na hudu na mayakan Boko Haram 81 da take nema ruwa a jallo, ciki har da Abubakar Shekau da Abu Mus’ab Al-Barnawi.

Kwamandan Rundunar Tsaro ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Farouk Yahaya ne ya bayyana hakan yayin jawabin maraba a sansanin sojoji na Chabbal dake birnin Maidugurin jihar Borno a ranar Laraba.

“Mun zo nan ne domin mu shaida kaddamar da rukuni na hudu na mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram karo na hudu. Kamar yadda kuka sani, wannan ba shine karo na farko ba, saboda haka nan ba da jimawa ba za mu kaddamar da wani rukunin,” inji Frouk.

Da yake jawabi, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum kira ya yi ga ‘yan ta’addan da su mayar da wukarsu cikin kube ta hanyar rungumar zaman lafiya.

Daga nan ne gwamnan ya damkawa Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai fastar dake dauke da sunaye da hotunan wadanda ake farautar.

Daga cikin wadanda ake neman akwai Abubakar Shekau da Abu Mus’ab Al- Barnawi da Modu Sulum da Umaru Tela da Iman Balge da Abu Umma da Mallam Bako (Hisbah) da Abu Dardda da Ibrahim Abu Maryam da wasu da dama.