✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram sun kai mana hari 72 —Al’ummar Chibok

Boko Haram ta kai hari a yankin na Chibok fiye da sau 72 tare kuma da kashe fiye da 407

Al’ummar Karamar Hukumar Chibok da ke Jihar Borno sun koka bisa ga yadda a cewarsu gwamnati ta yi watsi da su wanda hakan ya sa su fakawa cikin hare-haren Boko Haram tun shekarar 2014.

Wannan yanki na Chibok yanki ne da ya yi suna tun ranar 14 ga watan Afrilun 2014 lokacin da ’yan Boko Haram suka kwashe dalibai a makarantar ’yan mata ta GGSS Chibok su sama da 270.

A taron da suka gudanar a garin Abuja, Kungiyar Kula da Raya Yankin Chibok ta Kasa (KADA) ta bayyana a cikin bayaninta na bayan taro cewa akalla Boko Haram ta kai hari a yankin na Chibok fiye da sau 72 tare kuma da kashe fiye da 407 cikin wadannan hare-hare.

Kungiyar ta kara da cewa fiye da mutum 333 ne aka yi awon gaba da su tare da kona coci-coci fiye da 20 gidaje kuwa babu adadi tare da dukiyoyi.

Wannan taro na al’ummar Chibok dai an yi shi ne karkashin jagorancin shugabanta na kasa Dauda Iliya.

Dauda Iliya ya ce: “Za mu yi amfani da wannan dama a madadin dukkan al’ummarmu na Chibok don yin kira da babbar murya ga Mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kawo dauki ga al’ummar Chibok a kokarin da Boko Haram ke yi na mayar da su tamkar ba ’yan kasa ba ganin an yi watsi da kiyaicinsu.”

Shugaban ya kara da cewar, “Tun lokacin da aka sace ’ya’yanmu kimanin 276 a makarantar ta Chibok a shekarar 2014, har zuwa yanzun nan da muke magana muna da yara ’yan mata kimanin 110 da ke hannun wakannan mutane.

“A halin da ake ciki al’ummar wannan yanki na Chibok a kullum na ci gaba da fuskantar hare-hare da ke haifar da rasa rayuka da dauki dai-dai da ake mana da sauran ayyukan ta’addanci daga ’yan Boko Haram ba tare da daukar wani matakin kare mana rayukanmu ba daga bangaren gwamnati.

“Kai tsaye za mu iya cewa mu al’ummar Chibok karara gwamnatin kasar nan ta yi watsi da mu ba tare da kokarin kare mana rayukanmu ba ta kowace fuska kuwa.”