✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta bindige ’yan gudun hijirar Najeriya 50 a Nijar

Sun yi ta dirka wa mutanen harsashi daga kusa suna kuma kona gidajensu

Akalla mutum 50 ne mayakan Boko Haram suka bindige daga cikin fararen hula ’yan Najeriya da ke gudun hijira a garin Tumuk da ke Jamhuriyar Nijar.

Mayakan na Boko Haram sun yi ta harbin mutanen daga kurkusa suna kuma kona gidajensu a kazamin harin na ranar Lahadi.

Yawancin ’yan gudun hijirar sun fito ne daga Karamar Hukumar Abadam ta Jihar Borno inda ayyukan kungiyar suka sa su yin kaura zuwa Nijar domin samun tsira.

Bayanai da Aminiya ta samu sun nuna ’yan Najeriya fiye da 40,000 ne ke zaman gudun Hijira a garin an Tumuk.

A watan Mayun bana ne wasu daga cikin ’yan gudun hijirar suka koma Abadam bayan wani hari makamancin wannan da kungiyar ta kai musu.

Harin na garin Tumuk na zuwa ne ’yan makonni bayan Boko Haram ta kashe manoman shinkafa a yankin Zabarmari da ke Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno.

A harin ne kungiyar ta yi wa manoman kisan gilla ta hanyar yankan rago wasu kuma ta fille musu kai bayan ta kama su a gonakinsu.

Harin ya wanda aka samu alkaluma mabambanta game da hakikanin mutanen da kungiyar ta kashe ya sha kakkausan suka a fadin duniya.

Shekara 11 ke nan kungiyar ke ci gaba da tayar da hankula a Jihar Borno da makwabtanta na Arewa maso Gabashin Najeriya da ma yankin Tabkin Chadi.

Ayyukan Boko Haram sun yi sanadin mutuwar dubban mutane, tilasta wa miliyoyi gudun hijira, da kuma ruguza harkokin ilimi, tattalin arziki da kuma ci gaba.