✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta harbi jirgin agajin Majalisar Dinkin Duniya

Mayakan Boko Haram sun bude wuta a kan jirgin agaji na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a yankin Damasak na Jihar Borno. Jami’in agaji na MDD…

Mayakan Boko Haram sun bude wuta a kan jirgin agaji na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a yankin Damasak na Jihar Borno.

Jami’in agaji na MDD a Najeriya Edward Kallon ya ce mayakan sun kashe wasu mutum biyu ciki har da dan shekara biyar, suka kuma jikkata wasu da dama a harin da suka kai yankin.

“An harbi jirgin agajin MDD da harsasai a lokacin harin, sai dai babu jami’an agaji a cikinsa a lokacin, sannan dukkan matukansa na cikin koshin lafiya”, inji sanarwar da ya fitar.

Ya ce MDD za ta dakatar da zirga-zirgar jiragenta na agaji a yankin, har sai ta “gana da gwamnatoci abokan huldarta domin kara tantance tsaron lafiyan ma’aikatan agaji”.

Jiragen masu saukar ungulu su ne MDD ke amfani da su wajen kai abinci da kayan agaji ga kimanin mutum miliyan 7.8 da ke cikin matsananciyar bukata a yankin Arewa maso Gabashin Najerirya.

Kimanin mutum 36,000 ne rikicin Boko Haram ya yi ajalinsu a yankin inda wasu fiye da miliyan daya kuma ke gudun hijira.