✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kai harin ba-zata a wasu rukunin gidaje a Borno

Maharan a da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kai  harin rokoki a kan Rukunin Gidajen 1,000 da ke Maidugurin, hedikwatar Jihar…

Maharan a da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kai  harin rokoki a kan Rukunin Gidajen 1,000 da ke Maidugurin, hedikwatar Jihar Borno, lamarin da ya haifar da fargaba ga mazauna rukunin gidajen.

Wata majiyaa rukunin gidajen ta ce maharan sun rika harba manyan rokokin ne a kan wasu wurare a yankin na Gomari mai tazarar kilomita hudu daga filin jirgin saman kasa da kasa da ke Maidugurin.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da wassu unguwar ta Gomari, sun shaida mata cewa harin ya rusa wasu gidaje a yayin da wasu ke nuni da cewa babu asarar rayuka.

Wata majiyar da ke kusa da rundunar sojojin runduna ta 33 (Artillery), da ke aikin samar da tsaro a garin Njimtelo a jihar, ta bayyana daukar zazzafan matakin bude wuta ga wani ayarin ’yan ta’addan a lokacin da suke kai-komo a wajen birnin a ranar Jumu’a tare da dafawar jiragen yaki.

Wani soja a rundunar NA 7 da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da harin tare da cewa, ’yan ta’addan Boko Haram/ ISWAP sun yi kokarin shiga garin Maiduguri ne a ranar Juma’a amma sojojin Operation Hadin Kai tare da taimakon jiragen yaki suka dakile yunkuri.

Wata mai kama da haka kuma an sake kwafsawa tsakanin sojoji da ’yan ta’addan ISWAP da suka yi yunkurin kai hari a wani sansanin soji da ke Kala Balge a Jihar, amma sojojin suka hallaka kimanin 20 daga cikinsu, wasu sojoji kuma suka kwanta dama.

Wata majiya ta bayyana cewa, an kai harin na Kala Balge ne da misalin karfe 1:30 na dare kafin wayewar garin ranar Jummu’a a garin Rann da ke da kan iyakar Najeriya da Kamaru.