✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe mutum 56 a Jamhuriyar Nijar

Maharan sun kuma jikkata wasu da dama a kauyukan Tchombangou da Zaroumdareye.

Gwamnatin Jamhuniyar Nijar ta ce akalla mutum 56 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare biyu da ’yan tada kayar baya suka kai.

Gwamnatin kasar na zargin mayakan Boko Haram ne suka kai farmakin a wasu kauyuka da ke makwabtaka da iyakar Mali da Nijar.

Kauyukan da aka kai harin Mali sun hada da Tchombangou da kuma Zaroumdareye.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Alkache Alhada, ya ce akalla mutum 56 sun rasu, sai kuma wasu sama da 20 da suka ji raunuka.

Ko a watan da ya gabata, Boko Haram ta kai hari tare da kashe mutane 50 daga cikin ’yan gudun hijira daga Najeriya, a garin Tumuk da ke Nijar.