✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe rabin malaman makarantun Arewa maso Gabas —NEDC

Babban Daraktan Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya (NEDC) Muhammad Alkali ya ce kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da kashi 50 cikin 100…

Babban Daraktan Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya (NEDC) Muhammad Alkali ya ce kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da kashi 50 cikin 100 na malaman makaranta a yankin.

Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron hukumar karo na 50, wanda kwamitin sadarwa ta shugaban kasa ya shirya.

Ya ce sauran malaman makarantar da ke yankin na cikin firgici, kasancewar hankalin mayakan Boko Haram din na kansu a kodayaushe.

“Babbar matsalar da ba ma a Najeriya kadai ba ake fama da ita, ita ce ta karancin malaman makaranta.

“A Kudu maso Gabas, fiye da kashi 50 cikin 100 na malaman an kashe su, wasu kuma wani abu ya faru da su sakamakon rikicin Boko Haram.

“Don haka muna tsananin bukatar malaman makaranta a yankin,” in ji shi.

Ya ce rashin ilimin Boko ya kara ta’azzara matsalar tsaro a Arewa maso Gabas, wanda ya tilas wa hukumar kafa asusun tallafa wa ilimin yankin.

“Yanzu haka muna kokarin tara Naira biliyan shida, kuma kashi 10 na kudin shigar da za mu samu za mu dinga sanyawa ne a asusun.