✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe soja 20 a Borno

Akalla soja 20 ne suka mutu a wani kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa tawagar motocinsu a jihar Borno. Mayakan kungiyar…

Akalla soja 20 ne suka mutu a wani kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa tawagar motocinsu a jihar Borno.

Mayakan kungiyar sun kashe sojojin ne a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, tare da jikkata wasu da dama a harin na ranar Talata, a cewar wata majiyar tsaro.

“An kwashi gawarwakin sojojin da suka mutu zuwa Maiduguri yayin da ake jinyar wadanda suka samu raunuka a wani asibitin soji”.

Majiyar ta ce sojojin na hanayrsu ta zuwa su kora ragowar ‘yan kungiyar ne, amma a hanya mayakan suka yi wa motocinsu lanmbo suka yi ta harbinsu ta kowace kusurwa.
Karin bayani na nan tafe…..