✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe sojoji 24 a Chadi

Boko Haram ta kashe fiye da mutum 36,000 cikin shekaru 12.

Sojojin kasar Chadi 24 aka kashe yayin wani hari da ake zargin mayakan ’yan ta’adda masu ikirarin jihadi ne suka kai a yankin Tafkin Chadi.

Bayanai sun ce sojojin da mayakan Boko Haram suka kai wa farmakin na tsaka da hutuwa ne bayan dawowa daga sintiri a ranar Laraba kamar yadda Mataimakin Shugaban Yankin, Haki Djiddi ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Djiddi ya ce sojoji 24 ne suka mutu yayin da kuma da dama suka jikkata, sannan wasu kuma suka waste cikin karkara.

Kakakin rundunar sojin Chadi, Janar Azem Bermandoa Agouna, ya ce an kai harin ne a Tchoukou Telia, tsibiri mai nisan kilomita 19 a Arewa maso Yamma da N’Djamene, babban birnin kasar.

Sai dai a yayin bayar da tabbacin faruwar lamarin a ranar Alhamis, Janar Agouna ya ki bayyana adadin rayukan dakarun sojin da suka salwanta.

Mayakan Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’adda sun jima suna amfani da yankin Tafkin Chadi tsawon shekaru a matsayin mafaka inda suke kai hari kan sojoji da fararen hula a yankunan Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi da ke iyaka da Tafkin.

A watan Maris na shekarar da ta gabata ce akalla sojojin Chadi 100 suka rasa rayukansu sakamakon wani harin dare a tsibirin Bohoma.

A kan haka ne tsohon Shugaban Kasar, Marigayi Idris Deby Itno ya kaddamar da gagarumin farmaki kan Boko inda ya yi ikirarin samun nasarar kashe mayakan kungiyar fiye dubu daya.

A watan Afrilun bana ne shugaba Deby ya rasa ransa yayin gwabzawa da wasu ’yan tawaye a Arewacin Kasar, inda dansa, Mahamat Idriss Deby ya maye gurbinsa a matsayin jagoran dakarun kasar.

Tun a shekarar 2009 ce Kungiyar Boko Haram ta daura damarar ta’addanaci a Najeriya wanda ya zuwa yanzu ya dawu a wasu kasashen da ke makotaka da kasar.

A cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya (UN), fiye da mutum 36,000 sun rasa rayukansu wanda galibi ’yan Najeriya suka fi rinjaye, yayin da fiye da mutum miliyan uku suka rasa matsugunansu.