✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kona asibiti da makaranta a Yobe

Sun kai harin a garin Katarko yayin da ake shirin Sallar Asuba.

Wasu maharan da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari garin Katarko da ke Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Wani mazaunin yankin, Garga Modu, ya tabbatar wa Aminiya cewa maharan sun kona makarantar firamare da cibiyar kiwon lafiya da ke yankin a harin da suka mamaye garin da alfijir yayin da ake shirin yin Sallar Asuba.

“Da muka ji karar harbe-harbe sai muka koma gidajenmu muka sanar da makwabtanmu kowa ya gudu domin tsira.

“Daga cikin dajin, da muka boye muka hangi wuta na cin makarantar, sai muka yi gaba, daga baya aka kira mu cewa sun tafi, sannan muka dawo muka samu sun cinna wa asibitin wuta.

“Mun kuma samu labarin cewa maharan sun nufi sansanin sojoji a yayin inda suka yi musayar wuta da su,” inji shi.

Babu labarin asarar rai daga bangaren mazauna; mun kuma kokarin samun bayani daga Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Operation Lafiya Dole da ke Damaturu, Laftanar Kennedy Anyanwu kan batun amma hakan ba ta samu ba.

Kwamishinan Kula da Ayyukan Jinkai na Jihar Yobe, Abubakar Iliya, ya ce ya ziyarci yankin don jajanta musu a madadin Gwamnatin Jihar, tare da tantance irin barnar da aka yi.