✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta nada sabon shugabanci bayan mutuwar Shekau

Sahaba ya yi wa mayaka jawabi bayan tabbatar mutuwar Shekau.

Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da sabon shugabanci, bayan ta tabbatar mutuwar tsohon Shugabanta Abubakar Shekau.

Wani bidiyo da Boko Haram ta fitar da harshen Larabci, ya nuna daya daga cikin kwamandojinta, Bakura Modu, mai lakabi da Sahaba, yana kira ga bangarorin kungiyar da su kasance masu biyayya duk da rasuwar Shekau.

“Kar ku bari abin da ya same ku ya karya muku guiwa a jihadin da kuke yi, saboda Allah bai yi watsi da kokarinku ba,” inji shi, a cikin sakon da yake kira ga kwamandojin kungiyar.

Bidiyon ya nuna Bakura a tsakanin wasu mayaka a yayin da yake jawabi, a irin salon da kungiyar ta saba gabatar da sabbin shugabanninta.

Ya bukaci mayakan na Boko Haram da kar da su yi mubaya’a ga shugaban  kungiyar ISWAP, Abu Mus’ab Albarnawi a matsayin shugaba.

Kalaman na Bakura Modu a sabon bidiyon na Boko Haram da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu ya nuna har yanzu akwai rabuwar kai tsakanin bangarorin kungiyar ’yan ta’addan.

Majiyoyin tsaro sun ce tun bayan mutuwar Shekau rikici tsakanin kungiyoyin biyu ya karu, inda mayakan ISWAP suka kai hari tare da kame kwamandojojin Boko Haram da ba su mika wuya sun dawo cikinta ba.

A karshe dai ta tabbata Shekau, wanda aka jima ana kwan-gaba-kwan-baya kan kashe shi, ya mutu, a yayin artabu da mayakan kungiyar ISWAP mai mubaya’a ga kungiyar ISIS.

Ana ganin mutuwarsa matsayin sabon shafi a yaki da ta’addanci a Najeriya, inda ISWAP take kara karfi a yankin Arewa maso Gabas, cibiyar ayyukan ta’addancin da ya shafe shekara 12 yana ci wa kasar da makwabtanta tuwo a kwarya.

Shekau, wanda ya kara kaurin suna bayan sace dalibai kusan 300 a Makarantar Chibok, ya kashe kansa ne a watan Mayu, bayan mayakan ISWAP sun kai masa hari a maboyarsa da ke Jihar Borno.

Shugaban ISWAP, Abu Mus’ab Al-Barnawi, ya yi ikirari a cikin wani sakon murya cewa Shekau ya kashe kanshi ne domin guje wa mayakan ISWAP da suka ritsa shi.

Tun a shekarar 2016 ISWAP ta balle daga Boko Haram bisa zargin Shekau da kai hari barkatai a kan fararen hula da mata da kuma amfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake.

Bakura na daga cikin kwamandojoin Boko Haram a yankin Tabkin Chadi inda kungiyar take karakaina a kan iyakokin kasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar.