✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta sace mata hudu a Adamawa

Boko Haram ta sace 'yan mata uku da wata tsohuwa yayin da suke aiki a gona

Mazauna Karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa, sun bukaci a samar musu da tsaro, bayan sace ‘yan mata da kungiyar Boko Haram ta yi.

Madagali na daya daga ciki kananan hukumomi da Boko Haram ta mamaye a 2014 kafin sojoji su kwato garin a 2015.

“An sace mana yaranmu, muna kiran gwamnati da jami’an tsaro da su taimaka su ceto mana su,” cewar iyayen yaran.

Mutanen yankin sun bayyana cewa wasu mutane da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun sace ‘yan mata uku da matar aure yayin da suke aiki a gona a kauyen Dar a jihar.

Daga baya kuma ‘yan tada kayar bayan sun saki matar auren saboda tsufarta.

Wani mazaunin yankin, Iskarju Ezekiel, ya roki jami’an tsaro da su zakulo maboyar ‘yan tada kayar bayan a garin Madagali, wanda yake makwabtaka da Jihar Borno.

Mun yi kokarin jin ta bakin rundunar sojin ‘Aemoured’ da ke Yola kan lamarin, amma hakan ya faskara.