✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta sake kai hari Gwoza karo na biyu a watan Ramadan

Ya zuwa yanzu dai ba a san adadin mayakan da sojojin suka kashe ba.

Mayakan Boko Haram sun sake kai wani sabon hari a fafutikar da suke yi ta ganin sun kwace garin Gwoza da sanyin safiyar Lahadin nan, sai dai a wannan karon ma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

A Litinin din makon jiya ce mayakan suka kai hari garin Gwoza ana daf da yin buda baki, makonni biyu baya, kuma suka sake kawo harin, inda suka shigo ta kasuwar garin ana tsaka da ranar cin kasuwa.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya ta wayar tarho cewa, “a wannan karon sun yi wata dabara ne, inda suka rufe jikinsu da ciyawa, suna tafiya tamkar Shanu, har suka samu shigowa.”

A cewarsa, “jama’a da dama da suka fara baje hajarsu, sun tsere sun bar kayan nasu, sai dai Allah cikin ikonsa ’yan Boko Haram din basu samu nasara ba a yayin da sojoji suka yi gaggawar tunkarar lamarin.”

Ya zuwa yanzu dai ba a san adadin mayakan da sojojin suka kashe ba sakamakon ruwan harsasai da suka rika yi musu.

A baya bayan nan mayakan Boko Haram sun rika mika kansu ga jami’an tsaro a garin na Gwoza da sunan tuba, sai dai majiyar tamu ta ce akwai yiwuwar wasunsu tuban muzuru suke yi.

Majiyar ta ce bayan kwana biyu an samu daya daga cikin wadanda suka mika kai ga jami’an tsaro da sunan tuba da ya tsere.

An tabbatar da cewa wanda ya tseren ya kai wa sauran ’yan uwansu rahoto ne bayan liken asiri kan yadda garin yake.

Hakan na zuwa ne bayan jami’an tsaro suka samu nasarar cafke shi kuma ya bayyana wannan shiri da suke yi na ganin sun kafa tutarsu a garin Gwoza.