Boko Haram ta sake kai hari, ta yi ta’asa a garin Chibok | Aminiya

Boko Haram ta sake kai hari, ta yi ta’asa a garin Chibok

    Ishaq Isma’il Musa da Olatunji Omirin, Maiduguri

Kimanin fararen hula uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai hari wani kauye a Karamar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.

Majiyoyi sun bayyana cewa mayakan sun kai hari ne kauyen Kautikari da ke kusa da garin Chibok da misalin karfe 4.00 na yammacin Juma’a, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi sannan suka kone gidaje da dama.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan wadanda ba su fuskanci tirjiya ba sun kai harin ne a wasu motoci yaki biyar masu dauke da bindiogin harbo jiragen sama ba.

Majiyar rahoton ta shaida cewa mayakan sun shafe akalla awa biyu suna ta’asa inda suka rika bi gida-gida a kauyen suna banka musu wuta.

“Maharan da suke haye akan wasu motocin yaki biyar sun kutsa kai kauyen Kautikari sannan suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

“Mutum uku sun rasa rayukansu yayin da kuma suka kone gidaje da dama ciki har da wani coci da waa makaranta,” a cewar majiyar.

Bayanai sun ce mutanen kauyen sun ranta a na kare zuwa garin Chibok domin neman mafaka.