✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta sake kashe ’yan jari-bola 13 a Borno

’Yan jari bolan sukan shiga dazuzzuka daga garuruwa tsinto karafa ba tare da sanar da jami’an tsaro ba.

Mayakan Boko Haram sun sake kashe wasu ’yan jari-bola 13 a garin Goni Kurmu da ke Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wata majiyar leken asiri ce ta bayyana hakan yayin zantawa da wani masanin kan al’amuran da suka shafi yaki da tayar da kayar baya, Zagazola Makama, wanda kuma mai sharhi ne kan harkokin tsaro a yankunan Tafkin Chadi.

Majiyar ta ce mayakan sun kai harin ne a ranar Asabar inda suka yi wa ’yan kungiyar jari-bolan kofar rago a sakamakon shigar ba zata da suka ka yi musu ta wani gari da ake kira Gazuwa.

Kamar yadda majiyar ta shaida wa Zagazola Makama, harin ya sanya mutane da dama sun tsere ciki har da mata da kananan yara, wanda galibi ’yan gudun hijira ne da suka fake a garin Bama.

Bayanai sun ce mayakan na Boko Haram sun kai harin ne haye a kan motoci da babura, yayin da wasu da ke tafe a kafa, suka yi wa mazaunan kawanya.

Boko Haram dai ta sha kai hari kan masu sana’ar tarawa da fasa tsoffin karafa da ake kira ’yan jato ko ’yan jari-bola, sakamakon zarginsu da mayakanta ke yi da cewa suna satar kadarorin da aka yi watsi da su a cikin garuruwan da suka zama kufai.

Ana iya tuna cewa, a ranar 22 ga watan Mayu ne mayakan Boko Haram suka kashe ’yan jari Bola kusan 32 a kauyen Modu da ke Karamar Hukumar Kala-Balge da kuma wasu 23 a kauyen Mukdala na Karamar Hukumar Dikwa duk a Jihar Bornon.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan ’yan sanda Jihar Borno, Abdu Umar ya ce wadanda lamarin ya shafa galibi sukan shiga cikin dazuzzuka daga garuruwan tsinto karafa ba tare da sanar da jami’an tsaro ba.