✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Za a kara yawan sojojin sama a Borno

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta kara yawan dakarunta dake Maiduguri a ci gaba da yakin da ake yi da ta da kayar baya…

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta kara yawan dakarunta dake Maiduguri a ci gaba da yakin da ake yi da ta da kayar baya a Arewa Maso Gabas.

Babban Hafsan Rundunar Air Mashal Saddique Abubakar ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ga dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito babban hafsan yana cewa za a yi hakan ne da nufin kara wa dakarun karfi.

Ya kuma kaddamar da wasu ayyuka ciki har da dakunan kwanan sojoji, wadanda ya ce an samar da su ne saboda dakarun da za a karo.

“Kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta na hana ruwa gudu wajen ci gaban kasa; za mu kawar da shi ne kawai idan muka ci gaba da jajircewa a yakin da muke yi da ta da kayar baya da sauran miyagun laifuffuka”, inji Mashal Abubakar.

Ya kuma sha alwashin ganin matsalar karancin matsuguni a tsakanin sojojin sama ta kau.

“Fatana shi ne za ku ba da tukwicin [wannan aikin] ta hanyar yi wa ragowar mayakan Boko haram mummunar mahangurba.

“Ina bukatar ku da kada ku karaya yayin da muke ci gaba da fafatawa har sai kawar da masu ta da kayar baya kwata-kwata”, inji babban hafsan.