✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bom ya kashe mafarauta 7 a Borno

Mafarautan na sintiri ne lokacin da suka taka bom din da Boko Haram

Akalla mafarauta bakwai ne suka rasu, tare da konewar motoci biyu yayin da suka taka wani bom da kungiyar Boko Haram ta dasa a kan hanya.

Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata, a kauyen Kayamla da ke Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno.

Musa Bukar, daya daga cikin ’yan bangar, ya ce “Muna kan sintiri a yankin Kayamla, sai muka ji kara, mun dauka taya ce ta fashe, ashe bom ne muka taka.

“Abun takaici shi ne mun rasa mutum bakwai daga cikin abokan aikimu, sai daya da ya ji rauni. Yanzu haka yana Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ana kula da shi,” cewar Bukar.

Ya kara da cewa an binne mutane bakwai da suma rasu a makabartar Gwange a safiyar ranar Laraba.