✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Bom’ ya kashe mutum 1, wasu 7 sun jikkata a gidan giya a Yobe

Bayan sallar Tarawi aka ji karar fashewar wani abu da ake zargin bom ne, wasu kuma na cewa tukunyar gas ce ta yi bindiga a…

Mutum daya ya rasu, wasu akalla bakwai kuma sun jikkata sakamakon fashewar wani abu a wani gidan giya a Jihar Yobe.

Bayan Sallar Tarawi ne dai aka ji karar fashewar wani abu da ake tunanin bom ne a garin Gashua da ke Karamar Hukumar Bade a jihar ta Yobe.

Hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya wasu bakwai suka ji raunuka da kuma karaya.

Sai dai kuma wasu mazauna garin sun bayyana cewa tukunyar gas ce ta fashe a gidan wata amarya, ba bom ba.

Faruwar lamarin dai ya jawo hankalin Shugaban Karaman Hukumar ta Bade, Sanda Kara Bade, ziyartar wajen da abin ya faru tare da jami’an tsaro don gane wa kansa.

Shugaban ya dauki nauyin jinyar wadanda suka samu raunukan, wanda ya rasu kuma an kai gawarsa asibiti.

Nan take shugaban karamar hukumar ya kafa kwamitin gaggawa domin binciko hakikanin abin da ya faru sannan ya ba da umarni a rufe mashayan da ke garin na Gashua

Cikakken bayanin zai biyo baya.