✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bom ya kashe mutum 100 a Somaliya

Shugaban Kasar Somalia, Hassan Sheikh Mohamud ya tabbatar da cewa akalla mutum 100 ne aka kashe sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake biyu da aka…

Shugaban Kasar Somalia, Hassan Sheikh Mohamud ya tabbatar da cewa akalla mutum 100 ne aka kashe sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake biyu da aka kai da motoci a wajen Ma’aikatar Ilimi ta kasar.

An kai harin ne a ranar Asabar a Mogadishu, babban birnin kasar, inda akalla mutum 300 suka samu raunuka daban-daban.

Mista Mahmud ya kai ziyara wurin da aka kai harin inda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana cewa cikin mintoci kaɗan motocin suka kaddamar da hare-haren.

Shaidu sun bayyana cewa ita motar ta biyun ma ta kai harin ne a yayin da jama’a suka garzayo da kuma motar daukar marasa lafiya domin kai agaji.

Babu wata kunigiya da ta dauki nauyin kai harin zuwa yanzu amma kungiyar al-Shabab da ke da alaka da Al-Qaeda ta sha kaddamar da irin wadannan hare-hare.

Kungiyar ta al-Shabab ta yi sanadin mutuwar dubban mutane a kasar ta Somalia da kuma raba miliyoyi da muhallansu.

A ’yan kwanakin nan gwamnatin kasar ta rika zafafa hare-hare kan ’yan kungiyar, lamarin da ya jawo ita ma kungiyar ke zafafa hare-hare.

Ko a kwanakin baya sai da kungiyar ta kai hari a wani otel inda ta kashe mutane da dama.