✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bom ya kashe mutum 20, ya jikkata da dama a Afghanistan

Bom din ya tashi ne a wuri mai tsananin tsaro.

Akalla mutum 20 sun mutu, sannan da dama sun jikkata sakamakon tada bom da wani dan kunar bakin-wake ya yi a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Rahotanni sun ce bam din ya tashi ne a kusa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ranar Laraba.

Jami’i a Ma’aikatar Yada Labarai ta gwamnatin Taliban, Ustad Fareedun, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, dan kunar bakin-waken ya so ta da bam din a cikin ma’aikatar ne amma hakan bai samu ba.

Ya ce akalla mutum 20 suka mutu, yayin da wasu da dama sun jikkata sakamakon harin.

Kakakin ’yan sandan Kabul, Khalid Zadran, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa inda abin ya auku.

Harin ya auku ne ranar Laraba da misalin karfe 4:00 na rana agogon kasar, daidai da karfe 11:30 agogon GMT, in ji Zadran.

Sai dai, ya zuwa hada wannan rahoton jami’an Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da ta harkokin wajen kasar, ba su ce komai ba game da fashewar.

Malami a Jami’ar Amurka da ke Kabul, Obaidullah Baheer, ya ce abin tashin hankali ne adadin wadanda tashin bom din ya ritsa da su.

“A baya mun ga ‘yan Taliban sun aikata irin haka. Sam, bai taimaka wa sha’anin tsaro boye ainihin adadin mutanen da suka mutu.

“Bom din ya tashi ne a wuri mai tsananin tsaro inda ake da shingen bincike da dama, kai, sai da izini kafin ka bi wannan hanyar,” kamar yadda malamin ya shaida wa kafar Al Jazeera.

Bayanai sun ce bom din ya tashi ne yayin da wata tawagar China ke tsaka da tattauna da Taliban a Ma’aikatar ta harkokin wajen kasar.