✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya kashe yara 5 a Afghanistan

An yi nasarar tono wasu karin bama-bamai guda biyu da ba su kai ga fashewa ba.

Kimanin yara guda biyar sun rasa rayukansu a sakamakon wasu ababen fashewa da suka tarwatse a wurare biyu a birnin Herat na Afghanistan.

Rahotannin da DW ta samu na cewa akwai wasu mutane 20 da ababen fashewar suka jikkata.

Hukumomin Taliban masu mulkin Afghanistan sun ce lamarin ya faru ne a ranar Jumma’a, lokacin da kananan yara suka tono ababen fashewar, suka fara wasa da su.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin tayar da bama-baman.

Sai dai Taliban ta ce ta yi nasarar tono wasu karin bama-bamai guda biyu da ba su kai ga fashewa ba a kusa da wurin da lamarin ya faru a ranar Jumma’a.