Bonono rufe kofa da barawo! | Aminiya

Bonono rufe kofa da barawo!

    Abdulkarim Daiyabu

Ana murna bako ya tafi ashe mugun yana bayan gari. Ana murna Buhari zai zo ya yi mana maganin barayin gwamnati ashe sun tanadi maganinsa a fadar Shugaban Kasa, maimakon ya yi maganin ’yan kungiyar asiri, wakilansu da ake kira da kabal sun yi maganinsa.

Maimakon jami’an gwamnati su zamo masu hidima ga jama’a, sai suka zama masu bautar da jama’ar a Najeriya.

Arzikin kasa da tsaro sun kare a tsakanin masu mulki da manyan ma’aikatan gwamnati, ba a maganar siyasa ko wata dimokuradiyya ko ci gaban kasa da al’ummar kasa.

Tunda sojoji suka kwace mulki da siyasa shi ke nan ta faru ta kare an yi wa mai dami daya sata.

Tunda aka kashe su Firayi Minista Sa Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato duk wani ci gaban Najeriya ya fara komawa baya.

Najeriya ta faro da kera makamai tare da kasashen Brazil da Indiya, su tuni sun ci gaba wajen kera makamai da jiragen sama da na kasa da na ruwa da na karkashin ruwa da makamashin Nukiliya da manyan injuna na kowace irin masana’anta da sauransu, yayin da mu sojoji suka mayar da namu kamfanin ya koma na yin kujeru.

Sa Ahmadu Bello ya biya Fam miliyan 53, kan za a jawo mana teku zuwa Arewa, tunda aka kashe shi har yau tekun ba ta shigo Arewa ba duk da kasancewa an samu ’yan Arewa takwas da suka yi mulkin kasar a bayan rasuwar Sa Ahmadu Bellon.

Babu addini ba al’ada ba adila. Bayin al’umma su zama su ne iyayen gidan al’umma? Wannan abu sai a Najeriya! Ina mutanen kirki daga cikinmu, masu ilimi da hankali da mutunci da imani?

Idan ba kasar marasa hankali ba wace kasa ce a kowace shekara sai ta ciwo bashi a kasafin kudinta, barayin shugabanni suna sacewa, suna kai wa kasashen da aka ciwo bashin ajiya?

Har kudin ruwa da ake biya ya wuce kashi 90 na adadin kudin da da aka ciwo bashin.

Ga biliyoyin daloli da yawansu ya wuce kasafin kudin Najeriya na shekara 25 a hannayen barayin gwamnati, shugabanni da ministoci da gwamnoni da jakunan barayin gwamnati an kasa ko an ki a kwato mana.

Tun farkon kafa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu ya ce, duk gwamnoni 36 barayi ne, shugabannin kananan hukumomi 774 barayi ne.

Ya zargi wadansu tsofaffin shugabannin kasa da sata, ya fara da ba da misali da shugabannin kananan hukumomi da aka fara kamawa aka tsare su da Gwamna James Ibori ya kawo batun dukiyar Abacha kuma ya yi misali da Dala biliyan 12.2 na lokacin Yakin Tekun Fasha (Kwamitin Pious Okigbo kan CBN) da Dala biliyan 16 na wutar lantarki da Dala biliyan 49.8 da aka soma ragewa, ga Dala biliyan 20 na gurbataccen mai a zamanin Ebele Jonathan da sauransu.

Tsohuwar Shugabar EFCC, Farida Waziri ta taba cewa duk shekara ana sace mana Dala biliyan 10 ana boyewa a bankunan wasu kasashe. Ke nan a shekara goma an sace mana Dala biliyan 100 an boye a waje.

Kafin EFCC, akwai wani marubuci dan Amurka mai suna Jeffrey Robinson da ya rubuta littafi mai suna The Sink, a cikin littafin ya ce, daga cikin Dala biliyan 120 da shugabanni marasa amana suka sace suka fitar zuwa wasu kasashe ana zargin tsohon Shugaban Soji Janar Ibrahim Babangida ya mallaki Dala biliyan 20 lokacin yana Shugaban Kasa daga 1985 zuwa 1993.

Hanyoyin samun labarai na kasa da kasa (international sources of information) sun ce adadin kudin da ake zargin IBB ya sace daga asusun Najeriya ya wuce Dala biliyan 35.

Akwai bukatar a yi bincike na kwakwaf a kwato dukiyar in hakan ya tabbata gaskiya. Sai maganar gona da dakin karatu da Obasanjo ya gina yana gwamnati.

Sai kuma marigayi Dikko Inde na Kwastam da marigayi Isma’ila Isa Funtuwa da dukkan mambobin Kabal da dukkan rahotannin baya wadanda ba a aiwatar da hukunce-hukuncen da suka kunsa ba, na rushewar bankuna.

Ga biliyoyin daloli da suke hannun Dizeini Maduake, tsohuwar Ministar Mai, an ce yawansu ya wuce kasafin kudin Najeriya na shekara biyar, ga kudin aikin Mambila shekara da shekaru ana ware kudi har yanzu ba a fara aikin ba.

Sannan kullum ana sayar da danyen mai ganga miliyan biyu da rabi ko fiye, wani lokaci har a kan Dalar Amurka 140 ko fiye a kowace ganga, ga yawan kara kudin fetur da kananzir da dizal da man jirgin sama ga yawan haraji a gida Najeriya, amma ake ta ciwo mana bashi.

Ga sayar da kadarorin gwamnati da rusa darajar Naira da bankuna da masana’antu da ma’adanai da noma da kiwo da sana’o’in hannu da fatauci da kasuwanci da tsaro da siyasa.

Abubuwa sun lalace sun tabarbare saboda lalacewar harkar shari’a da tozarta mulki da shugabanci da tsaro da tattalin arziki da siyasa.

Ina mafita? Mafita ita ce, mu rabu da kowa mu koma ga Allah, duk wani saba wa Allah da kowanenmu yake yi ya daina, ya tuba ga Allah da niyyar ba zai sake yi ba.

Musamman zina da luwadi da madigo da tauye ma’auni da algus da rashin cika alkawari da kin fitar da zakka da sauransu.

Kuma mutane kwararru adalai masu tsoron Allah da tausayin bayin Allah musamman malaman addini da ’yan siyasa farar hula zalla da ba su taba aikata mugun laifi ba, masu imani da mutunci su hada kansu, su tashi tsaye haikan har sai sun tabbatar gwamnati ta kafa wani kwamiti mai karfi, wanda zai binciki duk wanda ya taba rike kowane mukami na amanar jama’a tun daga 1985 zuwa lokacin da kwamitin zai fara aiki, ya zazzage kowa, gida da waje, kudi da kadara.

Duk abin da kowa ya mallaka ba bisa ka’ida ba a kwato mana, a bai wa kowa hakkinsa nan take, a hukunta duk masu laifi a bainar jama’a. A nuna a talabijin na kasa da na kasashen duniya.

Kowa ya ga makomar azzalumai da barayi, fajirai da yan kungiyar asiri da matsafa da bokaye da maciya amanar kasa da makiya Allah, makiya bayin Allah.

Duk wanda bai bayar da gudunmawa ga wannan gagarumin aikin Allah ba, shi ma abin zargi ne.

Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Aikin Gona ta Jihar Kano. 08023106666, 08060116666