✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boris Johnson ya sauka daga Firaministan Birtaniya

Hakn ya biyo bayan matsin lambar da yake fuskanta

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, ya sauka daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar Conservative a daidai lokacin da gwamnatinsa ke fuskantar tangal-tangal.

Gwamnatin kasar dai ta sha fama da ajiye aikin Ministoci da dama ranar Alhamis, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta rawaito.

Boris Johnson dai ya fuskanci matsin lamba ne kan ya sauka daga mukaminsa, a daidai lokacin da sabuwar Sakatariyar Ilimin kasar, Michelle Donelan da Sakataren Arewacin Ireland, Brandon Lewis, suka sauka daga mukamansu.

Kazalika Ministoci Helen Whately da Damian Hinds da George Freeman da Guy Opperman da Chris Philp da kuma James Cartlidge duk su ma sun ajiye mukaman nasu.

Sai dai Boris Johnson zai ci gaba da zama a kujerar Firaministan har zuwa lokacin da jam’iyyar tasa ta Conservative za ta zabi sabon shugaba.

Ana dai zargin Mista Johnson ne da karya dokoki, musamman wadanda suka shafi yin biki lokacin dokar kullen annobar COVID-19.