✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boris Johnson ya yi faduwar bakar tasa — Rasha

Sun ce alhakin rikicin Ukraine zai ci gaba da bibiyarsa

’Yan siyasar kasar Rasha sun yi murna da murabus din da Boris Johnson ya yi daga mukaminsa na Firaministan Birtaniya, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya yi faduwar bakar tasa.

A sakonninsu daban-daban, sun kuma yi Allah-wadai kan irin rawar da suka ce ya taka wajen goyon Ukraine a yakin da take fafatawa da kasarsu.

A ranar Alhamis ce Boris Johnson ya sanar da ajiye mukamin nasa bayan ministocin gwamnatinsa sun yi ta ajiye mukamansu sakamakon badakalolin da ake zarginsa da su.

Hatta Fadar Gwamnatin ta Rasha ta ce ta ji dadin faduwar da Boris din ya yi.

Jim kadan da sanarwar saukar ta Boris, Kakakin gwamnatin ta Rasha, Dmitry Peskov, ya ce, “Ba ya sonmu, mu ma ba ma son shi.”

’Yan Rasha dai sun yi ta sukar lamirin Mista Boris wanda a kwanan nan ya shaida wa takwarorinsa cewa yana so ya fi tsohuwar Firaminista, Margaret Thatcher, dadewa a kakn karaga.

Margaret dai ta shafe shekara 11 ne a kan mulkin Birtaniya daga shekarar 1979 zuwa 1990.

A cewar fitaccen attajirin nan na Rasha, Oleg Deripaska, Boris, wanda ya ce tamkar dan wasan kwaikwayo ne, ya yi faduwar bakar tasa, kuma alhakin dubban mutanen da yakin Ukraine ya shafa zai ci gaba da bibiyarsa.

Shi kuwa Shugaban Majalisar Rasha, Vyacheslav Volodin, cewa ya yi, “karshen wanda ya kware a barkwanci ya zo.

“Yana daya daga cIkin mutanen da suka rura wutar rikicinmu da Ukraine. Ya kamata sauran shugabannin kasashen Turai su tsaya su yi karatun ta-natsu a kan manufofinsu,” inji shi.

Ita kuwa wata kusa a Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova, ta ce faduwar ta Boris alamar irin karshen da kasashen na Yamma za su yi ce, wacce za ta kasance cike da rikice-rikicen siyasa da akida da kuma na tattalin arziki.

Ta ce, “Babban darasin da za a iya koya daga nan shi ne; kada ka nemi ganin bayan Rasha, don ba za ka yi nasara ba, sai dai ma ka karya hakoranka a kokarin yin hakan, bakinka ya koma wawulo,” inji Maria.