✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Borno ta Tsakiya: Kotu ta kori dan takarar Sanatan PDP

An maka dan takarar kan rashin shiga zaben fid-da-gwanin jam'iyyar a jihar.

Kotun Tarayya da ke zama a Maiduguri ta soke Mohammed Kumalia daga takarar Sanatan Borno ta Tsakiya a Jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Kotun ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke sunan Kumaila, wanda dan majalisar tarayya ne har sau biyu, saboda bai shiga zaben dan takarar kujerar da jam’iyyar da gudanar ba.

Jam’iyyar ta sanar da shi a matsayin dan takararta, bayan rade-radin janyewar Jubril Tatabe daga zawarcin takarar.

Sai dai Tatabe ya je kotu yana zargin wasu ne suka rubuta takarardar janyewarsa tare da satar sanya hannunsa; duk da haka, INEC ta ayyana Kumaila a matsayin dan takara.

Mista Tatabe ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan cire sunansa da INEC ta yi, yana neman ta kwato masa hakkinsa da yake zargin wasu masu fada a ji na jam’iyyar sun kwace.

Ita ma jam’iyyar APC a Jihar Borno, ta je Babbar Kotun Tarayya da ke Maiduguri domin kalubalantar takarar Kumalia, wanda bai shiga zaben fid-da-gwanin da Kaka-Shehu Lawan, tsohon Atoni-Janar na Jihar Borno ya lashe ba.

Alkalin kotun Jude Dagat, ya ce INEC ta yi kuskure kuma ba ta da hurumin karbar sunan dan takarar da bai shiga zaben fid-da-gwanin ba, sannan PDP ba ta da ikon tura sunan Kumalia.

Alkalin ya haramta wa Kumaila ikirarin takarar sannan ya ware ranar Talata 10 ga watan Janairu don yanke hukunci kan karar da Tatabe ya shigar.

Ko da aka tuntubi Mista Kumaila kan batun, ya ce zai jira hukuncin karar da Tatabe ya shigar kafin ya yi tsokaci.