✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Borno: Zulum ya ziyarci iyalan wadanda Boko Haram ta kashe a Kala-Balge

Gwamnan ya kai ziyarar ce ranar Lahadi domin yi musu ta'aziyya

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci Rann hedikwatar Karamar Hukumar Kala-Balge da ke Jihar domin jajanta wa iyalan mutum 32 da mayakan Boko Haram/ISWAP suka kashe a kwanakin baya. 

Aminiya ta ruwaito cewa yadda aka kashe mutum 32 sakamakon kwanton-baunar da aka yi musu  a kauyen Mudu da ke karamar hukumar Dikwa a Jihar, wanda ke da tazarar kilomita 45 daga Rann.

A cewar rahoton, ana kyautata zaton an harbe wadanda aka kashen ne a kusa da wajen.

Gwamna Zulum wanda ya ziyarci garin na Kala-Balge tare da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar, Dige Muhammed, wanda ya fito daga yankin da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Bama, Ngala da Kala-Balge, Dr Zainab Gimba, da tsohuwar Kwamishinan  Manyan Jami’o’i da Kimiyya da Fasaha da Kere-kere, Dokta Babagana Mustapha, ya kuma gana da ’yan uwa inda ya mika ta’aziyyarsa.

Gwamnan wanda ziyarar da ya kai Kala-Balge ita ce ta bakwai cikin shekara uku, ya bukaci mazauna yankin da su daina zuwa kauyukan da ba kowa ciki musamman domin tonon tsoffin karafa.

Ya ce ’yan ta’adda na neman kayan aiki iri daya kuma suna iya yin kwanton bauna a irin wadannan kauyuka da ba kowa ciki.

Gwamna Zulum a yayin ziyarar ya gana da kapin Mohammed Haruna Jibrin, kwamandan rundunar soji a Kala-Balge, da ke da hannu a ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da masu tada kayar baya.

A lokacin da yake garin Kala-Balge, gwamnan ya duba muhimman ababen more rayuwa tare da bayyana karin albashin ma’aikatan lafiya da ke zaune a babban asibitin Rann da kashi 100.

“Duk wani ma’aikacin lafiya da yake son yin aiki a nan, za mu rubanya albashin sa, kuma za mu tabbatar da cewa, Insha Allahu an samu sauyi na yau da kullum don ba su damar ziyartar iyalai,”

Zulum ya kuma ba da wa’adin watanni biyu na bude asibitoci da makarantu da aka kammala tare da kammala duk wani aiki da ake yi a Rann, hedikwatar karamar hukumar Kala-Balge.

Gwamnan ya kuma nuna takaicin rashin wasu abubuwan more rayuwa a hedikwatar Karamar Hukumar.