✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bude makarantu: An horas da malaman Gombe kan kariyar COVID-19

Za a bude makarantun firamare da sakandare ranar Litinin 5 ga Oktoba, 2020

A shirye-shiryenta na bude makarantun firamare da sakandare bayan kullen COVID-19, Jihar Gombe ta horas da shugabannin makarantu a kan matakan kariyar kamuwa daga cutar.

Hukumar kula da Ilimin Bai Daya ta jihar ta ce horaswar za ta ba wa shugabannin makarantun kwarewar da ta dace domin tabbatar da aiwatar da matakan kariyar cutar da kuma kula da dalibai idan aka bude makarantun.

A ranar Litinin 5 ga Oktoba, 2020 ne za a bude makarantun firamare da kuma manya da kananan sakandare da fadin jihar ta Gombe.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban hukumar, Babaji Babadidi, ya bayyana aniyar gwamnatin jihar na kula da jin dadin malamai da kuma aiwatar da karin girmansu da aka shafe shekaru ba a yi ba.

Ya ce gwamnain jihar ta riga ta kafa kwamitin zakulowa da kuma tantance malamai da suka cancanci karin girma sannan a shirye take ta aiwatar da dukkannin shawarwarin kwamitin.