✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bude Makarantu: Gwamnatin Tarayya ta yi wa jihohi gargadi

Kwamitin Yaki da COVID-19 na Fadar Shugaban Kasa ya gargadi jihohi game da shirinsu na bude makarantu da gidajen kallo da wuraren motsa jiki da…

Kwamitin Yaki da COVID-19 na Fadar Shugaban Kasa ya gargadi jihohi game da shirinsu na bude makarantu da gidajen kallo da wuraren motsa jiki da sauran wuraren taruwar jama’a.

Hakan na zuwa ne yayin da kwamitin ke kokawa bisa yadda ya ce ake wa dokokin kare yaduwar cutar COVID-19 hawan kawara a jihohi.

Shugaba kwamitin Boss Mustapha ya nuna damuwa kan yadda ya ce ake keta dokokin a wuraren ibada da kasuwanni da gidajen kallo kafa da tashoshin ababen hawa.

Boss Mustapah ya kara da cewa zuwa yanzu ba a bin matakan kariya a wuraren taruwar jama’a. “Matsalar ta fi kamari a kasuwanni, da tashoshin mota da wasu wuraren ibada.

“Gwamnatin Tarayya ta ayyana matakan kariya da ya kamata a kiyaye sannan ta bukaci gwamnatocin jihohi su tabbatar ana bin su. Don hakan ina yin tuni a kan wannan”, inji Boss Mustapha.

Ya ce akwai yiwuwar sake yin duba a kan daukacin matakan kariya da Gwamnatin Tarayya ta saukaka.

“Yadda ake karya dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi abu ne da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin duk ka’idojin da aka ayyana an yi su ne domin kare lafiyar al’umma”, inji shi.