✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bude makarantun Kano sai ranar 10 ga Agusta

Jihar Kano za ta bude makarantu a fadin jihar a ranar 10 ga watan Agusta domin jarabawar karshe ta dalibai ajin karshe a makarantar sakandare.…

Jihar Kano za ta bude makarantu a fadin jihar a ranar 10 ga watan Agusta domin jarabawar karshe ta dalibai ajin karshe a makarantar sakandare.

Sanarwar na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta amince da bude wa daliban makarantu daga ranar Talata 4 ga watan na Agusta, bayan rufe su tun watan Maris da nufin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Za a yi wa makaranu 19,000 feshin magani a Najeriya.

Za A Bude Makarantun Kaduna 10 Ga Agusta

Jadawalin WAEC Ya Nuna Wariya Ga Musulmai – MURIC

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Muhamamdu Sanusi Kiru ya jihar ta sanay bude makarantun a ranar 10 ga Agusta ne domin ba wa Ma’aikatar Muhallinta isasshiyar damar yin feshin magani a makarantun kafin a bude su.

Ya yi kashedi cewa duk makarnatar da ta sake ta bude kafin ranar za ta yaba wa aya zaki.

A ranar 17 ga watan Yuli ne daliban na babban ajin sakanadare za su fara rubuta jarabawar WAEC ta kammala sakandare.

Kwamishinan ya kuma bukaci shugabannin makarantun gwamnati da masu makarantun kudi su yi amfani da mako guda din da gwamnatin jihar ta kara su kammala shirye-shiryen tabbatar da sun cika dukkan matakan kariyar cutar coronavirus a makarantunsu.

Ya kara da da kira garesu da su fitar da tsarin da zai bayar da damar yin aiki na awa hudu-hudu a kowane zango, da kuma tabbatar da bayar da tazara a cikin dakunan kwanan dalibai da dakunan gwaje-gwaje da dakunan karatu da kuma ajujuwa.

A cewarsa, gwamnatin jihar za ta dauki nauyin gwajin cutar coronavirus ga dukkan dalibai da ma’aikata da za su koma makaranta, kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta shardanta.

Za ta kuma tura jami’ai daga ma’aikatar lafiya ta jihar zuwa dukkannin makarantu domin auna zafin jikin dalibai da ma’aikata.

Sanarwar ta kuma bukaci masu makarantu a fadin jihar da su tanadi wurin killace masu cutar na wucin gadi, domin ajiye wadanda ake zargi da zargi da kamuwa da ita kafin a wuce da su zuwa cibiyoyin jinyar ta.