Budurwa ta yi wa mahaifiyarta gunduwa-gunduwa | Aminiya

Budurwa ta yi wa mahaifiyarta gunduwa-gunduwa

    Sagir Kano Saleh da Iniabasi Umo, Uyo

Wata budurwa da ta kashe mahaifiyarta ta kuma yi gunduwa-gunduwa da sassan jikin gawar ta shiga hannu.

Shaidu sun ce dubun matashiyar ya cika ne bayan da ta yi wa mahaifiyar tata kisan gillan a Karamar Hukumar Ikot Ekpene, Jihar Akwa ibom.

“Wannan budurwar ta yi wa uwarta gunduwa-gunduaw a Ikot Ekpene, har tana da bakin ce wa ’yan sanda su kai ta duk inda za su kai ta, ba ta damu ba”, inji wani ganau.

Shaidan ya rubuta haka ne a tare da bidiyon da ya wallafa na wadda ake zargin inda aka gan ta an yi mata daurin huhun goro an jefa ta a bayan a-kori-kurar ’yan sanda.

Bayan an kama, dattawan garin sun tilasta mata daukar sassan jikin mamaciyar a baho ta zaga gari domin zama izina ga masu irin dabi’ar.

Shaidu sun ce ko da ka maka budurwar, babu wata alamar da-na-sani ko kaduwa da ta nuna, har aka damka ta a hannun ’yan sanda.

Bayan kama budurwar, dattawan garin sun tilasta mata daukar sassan jikin mamaciyar a baho suka zaga gari da ita domin zama izina.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Akwa Ibom, Odiko Macdon ya tababtar wa Aminiya da aukuwar lamarin, kuma wadda ake zargin tana tsare a hannun rundunar.

Macdon ce akwai daure kai a ce diya ta yi wa mahaifiyarta haka, yana mai cewa za a yi mata gwajin kwakwalwa kafin a gurfanar da ita a kotu.

“Gaskiya ne labarin. Ta yi wa mahaifiyarta gunduwa-gunduwa, muna zargin akwa tabin hankalinta amma mu ba likitoci ba ne balantana mu ce tababbiya ce.

“Likitoci za su yi gwaji su tabbatar ko tana da hankali; amma yaya za a yi mutum mai hankali ta yi wa uwar da ta haife ta haka?

“Yanzu haka muna tsare da ita. Mun tattara gawar mamaciyar mun ajiye a dakin ajiye gawa; da zarar sakamakon gwaji ya fito za mu gurfanar da ita.

“Mun yi gwajin farko amma a mu zurfafa binciken sirri kuma da zarar an kammala za a gurfanar da ita a kotu”, inji Macdon.