✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Budurwar da ta jira saurayinta shekara 16 ya fito a gidan yari

Wata daya da haduwarsu aka kulle shi, amma ta jira shi, kafin ya fito ta gina musu gida

Wata budurwa ’yar kasar Palasdin da aka kulle saurayinta na tsawon shekara 16 a gidan yari ta jira shi har sun yi aure, inda kafin ya fito ta sayi fili ta gina musu gida.

Gwamnatin kasar Isra’ila ta yanke wa matashin mai suna Abdulhadi Shamshari hukuncin daurin shekara 16 a gidan yari ne bisa zargin zama dan rundunar mayakan Al-Aksa.

Abdulhadi ya ce, “Bayan na shiga kungiyar ne muka yi ta wasan buya da hukumomin Isra’ila, daga shekarar 2000 zuwa 2003, shekarar da aka tsare ni ke nan.”

– Wata daya da haduwarsu aka kulle shi

A lokacin da aka kulle shi a gidan yari, shakarun masoyiyar tasa mai suna Shadhi Ali 17 ne, kuma wata guda ke nan da haduwar masoyan.

Bayan an kulle shi, hukumomin gidan yari sun hana kowa kai mishi ziyara ko aika masa sako, sai ’yan uwansa na jini.

Ganin haka ne aka yi ta jan hankalinta cewa kar ta karar da kuruciyarta tana jiran mutumin da ba ta da tabbacin ko yana raye, ko kuma fitowarsa a raye.

Ta ce, “Ana ta ce min ni matashiya ce, bai kamata in jingina rayuwata a kan mutumin da aka yanke wa hukuncin daurin shekara 16 ba. Bai dace in karar da kuruciyata ina zaman jiran shi ba.

“Amma duk da haka maganganun ba su karya min zuciya ba, duk da cewa a lokacin shekaruna ba su fi 17 zuwa 18 ba.

“A lokacin da nake zaman jiran shi, abin da nake gaya wa mutane shi ne tsawon lokacin da zan yi ina jira bai dame ni ba. Abin da ya fi muhimmanci a wurina shi ne na zama ta Hadi ce, shi ma ya zama nawa,” inji Shadhi bayan sun yi aure.

 

– Shekara bakwai babu sadarwa

Yana tsare a gidan yari Shadhi ta kammala jami’a, har ta fara aiki, wanda tana farawa ta bude asusu, ta kuma kayyade wani kaso na albashinta da take ajiyewa a ciki a duk wata,.

Da kudin da ta tara ne ta sayi fili ta kuma gina katafaren gida, wanda idan masoyin nata ya fito zai aure ta su zauna a ciki.

Bayan daure Abdulhadi, sai da aka shekara bakwai ba tare da wata sadarwa tsakaninsa da ita ba, ko da ta hannun lauyansa ne.

Sai daga baya ta samu ta fara aika mishi da wasika da sunan mahaifiyarsa.

Abdulhadi ya ce, “Na dauki tsawon lokaci ban san halin da duniya ke ciki ba daga yari ba, sai lokacin da na samu wasikar, wadda ita ce ta kara ba ni kwarin gwiwa a zamana a kurkuku.”

– Jaddada soyayyarsu

Shadhi Ali ta ce, “Ba ni da wani zabi face rubutwa masa wasika ta hannun kungiyar agaji ta Red Cross, ita ma wasikar ina aikawa ne da suna mahaifiyarsa, saboda an hana shi hulda da kowa sai ’yan uwansa na jini.”

A cikin wasikar ce ta jaddada masa mastsayin kaunarsa a zuciyarta da kuma cewa tana jiran shi, ba ta kuma yanke kaunar cewa za su zauna tare a matsayin mata da miji ba.

Daga nan ne suka ci gaba da aika wa juna wasika, soyayyarsu ta zama sabuwa fil.

Bayan shekara bakwai yana tsare, suna musayar wasiku da kyaututtuka, a shekarar 2010 aka yi wa masoyan baiko; Daga nan ne hukumomin gidan yari suka fara ba ta damar kai mishi ziyara.

Ta ce a lokacin da ta kai mishi ziyarar farko, “A hanyar shiga ina ta sauri ina gudu, ina so in riga kowa shiga; Ai kuwashigata ke da wuya, sai na gan shi a gabana, abin kamar a mafarki, amma ya dan canza.”

– Yadda ta gina gidan

Bayan Shadhi ta fara aiki ne ta dora wa kanta alhakin gina musu gidan da za su zauna idan sun yi aure da masoyin nata.

“Hadi ya rika turo min wani kaso na albashinsa da hukumomin Palasdinu ke ba wa fursunoni, ni kuma ina tara abin da nake ajiyewa daga albashina.

“Na rika ce masa, rayuwarmu ta nan gaba ita ce ta fi komai muhimmanci, a haka muka tara kudin da ya kai har muka mallaki gidan kanmu,” inji ta.

Bayan Abdulhadi Hamshari ya kammala wa’adin zamansa a gidan yari, ne ya tarar da wannan katafaren gidan da masoyiyar tashi da ke jiran shi ta gina musu, wanda yanzu a ciki suke zaune.

– An sha biki

Bayan fitowarsa shekarar 2019, aka daura musu aure aka sha biki, inda bayan nan ne sashen Larabci na BBC ya zanta da su.

Shadhi ta ce, “A tsawon lokacin da yake kulle duk shekara idan ta zo sai in yi ta fatan za a yi mishi afuwa, ya fito mu yi aure.

“Kowace shekara, ina ganin ita ce za ta zama shekarata ta karshe a gidan iyayena; Wannan fatar ce ta sa na ci gaba da jira.”

Daga shafin Sashen Larabci na BBC…