✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ba ya fifita Katsina a kan sauran Jihohi —Masari

Bai taba yi wa Jihar wani abu ba da ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulki ba.

Shugaba Muhammadu Buhari bai taba fifita Jihar Katsina da ta kasance cibiyarsa wajen samar da ababen more rayuwa da ci gaban kasa a kan sauran jihohin kasar ba.

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ne ya bayyana hakan yayin gabatar da tattaunawar farko ta bude wata kungiyar Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a karshen makon da ya gabata.

Yayin tattaunawar bude kungiyar ta NAN Forum, Masari ya ce Buhari ya dauki dukkan jihohi 36 na kasar da kuma Babban Birnin Tarayya a matsayin daya.

Masari ya ce ya yi mamaki lokacin da wani gwamna ya yi zargin cewa Shugaban Kasa ya bai wa Jihar Katsina fifiko wajen rabon Kudaden da Asusun Gwamnatin Tarayya ya fitar wacce ta samu Naira biliyan 6.25 domin samar da burtalan kiwon dabbobi.

“Na yi dariya sosai kan wannan zargi, domin a shekarar 2017 mun nemi tallafin Naira biliyan 12.85 domin samar da burtalan kiwo a Jihar Katsina.

“Mun nemi tallafin ne daga Asusun Albarkatun Kasa domin samar da burtalan kiwon a wasu Kananan Hukumomi amma hakar mu ba ta cimma ruwa ba.

“A lokacin gwamnatin tarayya cewa ta yi mu je mu nemo Naira biliyan 6.25 da kanmu, amma a karshe sai a bana Gwamnatin Tarayya ta bamu wannan kudi da muka nema domin kaddamar da aikin.

“Shugaba Buhari dan asalin Jihar Katsina ne, amma bai taba yi wa Jihar wani abu ba da ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulki don kawai Jihar ta kasance mahaifarsa.

“Saboda haka ya kamata mu rika sara muna duban bakin gatari kan duk wata bukata da za mu shigar wa gwamnatin tarayya.

“Ya kamata mu rika la’akari da bin da gwamnati za ta iya da kuma wanda ba za ta iya ba,” a cewar Masari.