✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya biya ’yan bindiga kudin fansa —Obasanjo

Buhari ya sha gargadin gwamnoni a kan bude kofar yin sulhu da ’yan bindiga.

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da biyan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane kudin fansa.

Obasanjo ya yi jawabin ne ranar Laraba yayin karbar bakuncin wasu ’yan kungiyar kabilar Tibi, a dakin karatunsa na OOPL da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Shugaba Buhari ya saba gargadin mutane kan biyan kudaden fansa ga ’yan bindiga, inda ya rika gargadi gwamnoni kan kada su bude kofar da za ta karfafa wa ’yan bindiga gwiwa da sunan sulhu ko biyan su kudin fansa.

Sai dai a cewar Obasanjo, kafin gwamnatin Buhari, hatta gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ta rika zama a teburin sulhu da ’yan bindiga duk da sun musanta aikata hakan.

“Koyaushe gwamnati na biyan kudin fansa. Ba wannan gwamnatin kadai ba, ko a lokacin mulkin Shugaba Jonathan sukan biya kudin fansa, duk da sun musanta aikata hakan.

“Jonathan ko Buhari babu wanda zai musanta wannan kalaman,” inji Obasanjo.

Kazalika, Obasanjo ya nemi  gwamnatin Shugaba Buhari ta samar da wata hanya ta yin maganin ’yan bindiga da masu satar mutane tun da tana kalubalantar biyan kudaden fansa.

Tsohon shugaban kasar ya kuma nuna goyon bayan a yaki ’yan ta’adda don shawo kan matsalar tsaro da ta addabi jama’a.

Aminiya ta rawaito Obasanjo na daya daga cikin wadanda suka rika kiraye-kirayen ganin an kubutar da ragowar daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka a Jihar Kaduna da ’yan bindiga suka yi awon gaba da su kimanin watanni biyu da suka gabata.

A yammacin Laraba ne ragowar daliban 27 da ke hannun ’yan bindiga suka shaki iskar ’yanci bayan shehin malamin nan na addinin Islama, Sheik Ahmed Abubakar Gumi ya shiga lamarin.