BUHARI DA MUSLIM | Aminiya

BUHARI DA MUSLIM

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

201. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Abu Salmah dan Abdurrahman ya ba ni labari cewa: Lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wuta ta taba kaiwa kukanta ga Ubagijinta ta ce: Ya Ubangiji! Sashena yana cin sashe, sai aka yi mata izini da ta rika numfashi sau biyu (a shekara). Numfashi daya lokacin hunturu (sanyi), daya kuma lokacin bazara (zafi). Shi ne abin da  kuke ji daga mafi tsananin  zafi, kuma haka kuke samu na tsananin sanyin hunturu.”

202. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Abu Amir Al’akadi ya ba mu labari ya ce, Hammam ya ba mu labari daga Abu Jamratu Duba’iyyu ya ce: “Na kasance ina zaune da Dan Abbas a Makka sai ciwon massasara ya kama ni. Sai ya ce mini: Ka sanyaya ta da ruwan Zam-Zam. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wannan masassara tana daga hucin Jahannama, ku rika sanyaya ta da ruwa, ko ya ce: Da ruwan Zam-Zam.” Hammam ne ya yi shakka.

203. An karbo daga Amru dan Abbas ya ce: “Abdurrahman ya ba mu labari ya ce, Sufiyan ya ba mu labari daga babansa daga Ibayatu dan Rifa’ah ya ce: “Rafi’u dan Khadij ya ba ni labari ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Masassara daga hucin Jahannama ne ku sanyaya ta ga barinku da ruwa.”

204. An karbo daga Malik dan Isma’il ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari daga Urwatu daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ciwon masassara daga hucin Jahannama ne ku sanyaya ta da ruwa.”

205. An karbo daga Musaddad ya ce: “Daga Yahaya daga Ubaidullah ya ce, Nafi’u ya ba ni labari daga Abu Zinad daga A’araj daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wutarku wani yanki ne daga yanki saba’in daga wutar Jahannama. Sai aka ce: Ya Manzon Allah! Wannan ma ta isa ga kafirai. Sai ya ce: “Za a fifita da kamar yanki sittin da tara kowace da misalin (kwatankwacin) zafinta take.”

206. An karbo daga Kutaiba dan Sa’id ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru ya ce, Adda’u ya bayar da labari daga Safawan dan Ya’alah daga babansa cewa: Lallai shi ya ji Annabi (SAW) yana karatu a bisa mumbari da cewa, ’yan uwata: Za su rika kira ya Maliki!” (wato Mala’ika Malik mai tsaron wuta).

207. An karbo daga Aliyu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga A’amashi daga Abu Wa’il ya ce, an ce da Usama shin ko za ka je ga wane (Usman) ka yi masa magana (game da yadda yake shugabancin jama’a). Sai ya ce: Kuna ganin ban masa magana face sai na jiyar da ku, cewa: Lallai ni ina masa magana cikin sirri ba tare da na bude masa kofa saboda kada in kasance farkon wanda ya bude masa kofa ba. Kuma ba zan fada ga wani mutum da ya zamo shugabana cewa, lallai shi ya fi mutane alheri a bayan komai na ji shi daga Manzon Allah (SAW) sai suka ce: “Me ka ji shi yana cewa? Ya ce, “Na ji shi yana cewa: “Za a zo da mutum Ranar Kiyama a jefa shi cikin wuta har sai kayan cikinsa sun fito waje. Sai ya rika juyawa kamar yadda jaki ke juyawa bisa turkensa (kamar dawakin matse raken mazarkwaila). Sai mutanen wuta su taru a kansa suna cewa: Ai wane! Mene ne sha’aninka? Shin ba kai ne kake umurtarmu da kyautatawa ba, kuma kana hana mu miyagun ayyuka? Sai ya ce: “Na kasance ina umurtarku da kyautatawa ni kuwa ban aikatawa. Kuma ina hana ku game da mugun aiki amma ni ina aikatawa.”