BUHARI DA MUSLIM | Aminiya

BUHARI DA MUSLIM

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

239. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahaya ya ba mu labari daga Isma’il ya ce, Kaisu ya ba ni labari daga Ukba dan Umar da Abu Mas’ud ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya yi nuni da hannunsa ta wajen Yamen ya ce: “Imani na wannan wuri, amma ku saurara! Bushewar zuciya da kaushin fushi na ga kauyawa marasa kula addini masu yawan taguwa inda kahonnin shaidanu biyu suke a kabilar Rabi’atu da Mudar.”

240. An karbo daga Kutaiba ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Ja’afar dan Rabi’atu daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Idan kun ji carar zakara to ku roki Allah kyautarSa lallai shi ya gano mala’iku ne. Idan kuka ji kukan jaki to ku nemi tsarin Allah daga Shaidan, saboda shi ya ga wani shaidani ne.”

241. An karbo daga Is’hak ya ce: “Rauhu ya ba mu labari ya ce, Dan Juraij ya ba mu labari ya ce, Adda’u ya ba ni labari cewa: Ya ji Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan duhun dare ya lulluba to ku tsare yaranku saboda shaidanun aljanu suna watsuwa ne a wannan lokaci. Idan lokacin daren ya shude ku sake su. Amma ku rufe kofofinku ku ambaci Allah. Saboda Shaidan ba ya iya bude kofar da aka rufe da ambaton sunan Allah.”

242. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Wuhaib ya ba mu labari daga Khalid daga Muhammad daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “An taba rasa wadansu jama’ar Yahudawa, amma ba a san laifin da suka aikata ba. Ban ga abin da aka mayar da su face sun zama beraye, saboda haka idan aka sanya masu (berayen) nonon taguwa ba sa sha. Amma idan aka sanya nonon tumaki sai su sha. Sai aka bayar da labarin haka ga Ka’ab ya ce: “Shin kai ka ji daga Annabi (SAW) yana fadin haka? Na ce, “Na’am, ya fada mini haka ba sau daya ba.” Na ce, “Shin sai na karanta maka Attaura ce?” (Wannan labari Allah Ya bayyana shi cikin Alkur’ani cewa: Yahudawa an taba mayar da su aladu ne da birrai. Kuma Muslim ya ruwaito cewa: An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: “Yanzu birrai da aladu daga zuriyar Yahudawa suke? Ya ce, “A’a.”

243. An karbo daga Sa’id dan Ufair ya ce: “DanWahab ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba ni labari daga Dan Shihab daga Urwatu yana bayar da labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: Tsaka fasika ce, amma ban ji ya umarci a kashe ta ba.” Amma Sa’ad dan Abu Wakkas ya ambata cewa: “ Lallai Annabi (SAW) ya umarta da a kashe ta.”

244. An karbo daga Sadakatu dan Fadal ya ce: “Dan Uyainatu ya ba mu labari ya ce, Abdulhamid dan Jubair dan Shaiba ya ba mu labari daga Sa’id dan Musayyib cewa: Lallai Ummu Sharik ta ba shi labari cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya umarce ta da kashe tsaka.”

245. An karbo daga Ubaidi dan Isma’il ya ce: “Abu Usamatu ya ba mu labari daga Hisham daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Ku kashe macizai biyu, na farko dai mai zane biyu a gadon baya. Na biyu kumurci saboda na bata ido, dayan kuma na zubar da ciki (idan mai ciki ta gan shi).”

246. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahaya ya ba mu labari daga Shiham ya ce, Babana ya ba ni labari daga A’isha (RA) ta ce: “Annabi (SAW) ya umarta da a kashe kumurci ya ce, saboda yana kashe ido, kuma yana zubar da ciki.”