Buhari da Muslim | Aminiya

Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

Babi na Biyar:

Ambato Idris (AS) shi ne kakan baban Nuhu (AS). Kuma ana cewa shi ne kakan Nuhu (AS). Da fadar Allah Madukaki cewa: “Kuma Muka daukaka shi a matsayi madaukaki.” (K:19:57). Abdan ya ce, Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri – Hawwala Sanad- ya ce, Ahmad dan Salihu ya ce, Dan Anbasata ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Dan Shihab ya ce, Anas dan Malik ya ce: Abu Zarri (Allah Ya yarda da shi), ya kasance yana bayar da labari cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce:

“An bude rufin dakina lokacin da nake garin Makka sai Jibrilu ya sauko ya buda kirjina sa’an nan ya wanke shi da ruwan Zamzam. Sa’an nan ya zo da wata tasa ta zinari cike da hikima da imani ya zuba cikin kirjina, sa’an nan ya mayar ya dinke. Sa’an nan ya yi riko da hannuna ya taka da ni zuwa sama lokacin da muka isa ga saman duniya. Sai Jibrilu ya ce ga mai tsaron sama: Bude! Ya ce, wane ne wannan? Ya ce, “Jibrilu ne, ya ce, akwai wani tare da kai ne? Ya ce, “Muhammad ke tare da ni.” Ya ce, “Shin har an aika gare shi? Ya ce, “Na’am.” Sai ya bude lokacin da muka hau sama sai ga wani mutum gefen damarsa da wasu duffai (jam’in duhu) ta gefen hagunansa ma akwai duhu. Idan ya duba gefen dama sai ya yi dariya idan ya duba gefen hagunansa sai ya yi kuka. Sai ya ce, “Maraba da Annabin kwarai dan kwarai.’ Sai na ce, wane ne wannan ya Jibrilu?” Ya ce, ‘Wannan Adam ne, wannan duhun da ke damarsa su ne mutanen Aljanna.

Duhun da ke gefen hagunansa su ne mutanen wuta. Saboda haka idan ya duba dama sai ya yi dariya, idan kuma ya duba gefen hagun sai ya yi kuka. Sa’an nan Jibrilu ya taka da ni zuwa sama har sai da muka kai sama ta biyu, sai ya ce da mai tsaronta.

“Bude!” Mai tsaronta ya ce masa misalin na farko ya fada sai ya bude.” Anas ya ce: “Ya ambata cewa lallai shi ya hadu (samu) a cikin saman Idris da Musa da Isa da Ibrahim amma bai tabbatar mini da yadda masaukansu suke ba sai ya ce: “Lallai shi ya iske Adam a saman duniya, Ibrahim a sama ta shida.” Anas ya ce: “Lokacin da Jibrilu ya shude da Idris (AS) ya ce, “Maraba da Annabin kwarai dan uwan kwarai.” Sai na ce, “Wane ne wannan? Ya ce, “Idris ne wannan.” Sa’an nan na shude da Musa ya ce: “Maraba da Annabin kwarai dan uwan kwarai.” Sai na ce, “Wane ne wannan?” Ya ce, “Musa (AS) ne.” Sa’an nan na shude da Isa (AS) sai ya ce: “Maraba da Annabin kwarai dan uwan kwarai.’ Na ce, “wane ne wannan? Ya ce: “Isa (AS) ne.” Sa’an nan na shude da Ibrahim (AS) ya ce: “Maraba da Annabin kwarai dan kwarai.” Na ce, “Wane ne wannan?” Ya ce, “Wannan Ibrahim ne.”

Dan Hazmin ya ba ni labari cewa: Lallai Dan Abbas da Abu Hayyata mutumin Madina sun kasa ce suna cewa: “Annabi (SAW) ya ce, “Sa’an nan aka taka da ni har sai da na kai matsayin da nake jin motsawar alkaluma.” Anas da Dan Hazmin suka ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Sai aka farlanta mini salloli hamsin, na komo da haka har sai da na zo shudewa da Musa (AS), sai Musa ya ce mini me aka farlanta wa al’ummarka? Na ce, “An farlanta musu salloli hamsin.” Ya ce: “Koma zuwa ga Ubangijinka ka nemi sauki. Saboda al’ummarka ba za su iya aikata haka ba. “Sai na koma na nemi saukin Ubangijina aka rage rabinta (wani sashe).

Na koma zuwa ga Musa ya ce: “Koma ga Ubangijinka ya ambata misalinsa aka rage rabinta. Na koma ga Musa na ba shi labari ya ce, “Koma zuwa ga Ubangijinka lallai al’ummarka ba za su iya aikata haka ba. Na koma na rokar musu sauki. Sai aka farlanta biyar tana daidai da Sallah hamsin ba a musanya magana gaba gare ni. Da na koma zuwa ga Musa (AS), sai ya ce: “Koma zuwa ga Ubangijinka na ce, “Hakika ina jin kunyar Ubangijina. Sa’an nan na tafi har sai da na je ga Sidratul Muntaha launuka ya lullube ta ban sanin ko meee ce ita ba. Sa’an nan aka shigar da ni Aljanna sai na ga ratayarta na lu’ulu’u ne. Kuma turbayarta na kanshin turaren Miski.”