Buhari da Muslim | Aminiya

Buhari da Muslim

    Sheikh Yunus Is’hak Almashgool

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Shida:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kuma zuwa ga Adawa Mun aika da dan uwansu Hud, ya ce: Ya ku mutanena! Ba ku da wani abin bauta baicin Allah…” (K:7:65). Da fadarSa cewa: “Lokacin da ya gargadi mutanensa da Ahkaf,.. har zuwa fadarSa cewa: Kamar haka Muke saka wa masu kyautatwa.” (k:46:21-25). Da fadar Sa cewa: “Amma Adawa na hallaka su da iska Sarsar (mai tsananin karfin murya)….” (K:69:6-7).

276. An karbo daga Muhammad dan Ar’arat ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Alhakam daga Mujahid daga Dan Abbas (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “An taimake shi da iskar Saba (iskar gabashiya), an hallaka Adawa da iskar Dubur (yammaci).” Dan Kasir ya karbo daga Dan Uyainat daga babansa daga Abu Nu’aim daga Abu Sa’id (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Aliyu ya taba aikawa zuwa ga Annabi (SAW) da wasu zinari sai ya raba su a tsakanin mutum hudu. Na farkon Akara’u dan Habus Alhanzaliyyu sa’an nan Mujashi’u da Uyainat dan Badar Fazariyyu da Zaid Da’iyyu, sa’an nan wani daga cikin kabilar Bani Nahban da Alkamat dan Ulasat. Sai Kuraishawa da wadansu mutanen Madina suka yi fushi suka ce: “Yana bayar wa ga manyan Najad yana kyale mu?” (Annabi) Ya ce, “Ina neman jan hankalinsu ne.” Sai wani mutum mai budaddun idanuwa, mai manyan kunci da katon goshi, mai gautsin gashin gemu ya aske kansa ya zo ya ce: “Ka ji tsoron Allah ya Muhammad! Sai (Annabi) ya ce: “Wane ne zai yi wa Allah da’a idan ni na saba maSa? Allah Ya amintar da ni ga mutanen duniya amma kai ba ka amince mini ba?” Sai wani mutum ya tambaya game kashe shi (mutumin nan). (Mai ruwaya) ya ce: “Ina tsammani Khalid danWalid ne ya nemi izinin, sai (Annabi SAW) ya hana shi. Lokacin da ya juya sai (Annabi SAW) ya ce, “Lallai daga cikin wadanda za su biyo bayan wannan su ne wadansu mutane masu karanta Alkur’ani amma bai ketare makoshinsu ba. Za su rika shiga da fita cikin addini kamar yadda kibiya ke fita cikin jikin abin harbi (ta wuce babu jini tare da ita). Kuma za su rika yakar jama’ar Musulmi, za su rika barin masu bautar gumaka. Idan zan iske irin wadannan jama’a zan yake su kamar yakin Adawa.”

277. An karbo daga Khalid dan Yazid ya ce: “Isra’ilu ya ba mu labari daga Abu Is’hak ya ba mu labari daga Aswad ya ce: “Na ji Abdullahi ya ce: “Na ji Annabi (SAW) yana karatun Fahal min muddakir.”

Babi na Bakwai:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kuma zuwa ga Samudawa Mun aika da dan uwansu Salihu…” (K:7:73). Da fadarSa cewa: “Mutanen Hijri sun karyata…” (K:15:80).” Ma’anar Hijru wurin zaman Samudawa, amma kalmar Hijru na kayan noma suna nufin haramun ne. Saboda takaitawa muka bar sauran fassarar kalmomin sai a duba littafin Tafsiri (Kundi na7).

278. An karbo daga Humaidiyyu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Hisham dan Urwata ya ba mu labari daga babansa daga Abdullahi dan Zama’atu ya ce: “Na ji Annabi (SAW) ya ambaci wanda ya soke taguwar Salihu ya ce: “Wani mutum ne mai matsayi, mafadi cikin mutanensa (mai karfin fada a-ji cikin mutanensa) kamar Abu Zama’atu.”

279. An karbo daga Muhammad dan Miskin dan Alhassan ya ce: “Yahaya dan Hassan dan Habban Abu Zakariyya ya ba mu labari ya ce, Sulaiman ya ba mu labari daga Abdullahi dan Dinar daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) lokacin da muka sauka a Hijri (na Samudawa) lokacin Yakin Tabuka ya umarci da kada su sha ruwan rijiyarsu kada su shayar daga gare ta. Sai suka ce, “Hakika mun kwaba garinmu da shi kuma mun tara ruwan, sai (Annabi SAW) ya umarce su da su zubar da garin, kuma su zubar da ruwan.”

280. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas dan Iyad ya ba mu labari daga Ubaidullahi daga Nafi’u cewa: Lallai Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ba shi labari cewa: Lallai wadansu mutane sun taba sauka tare da Manzon Allah (SAW) a kasar Samudawa (Hijri) sai suka tara ruwa daga rijiyarsu suka kwaba gari da shi. Sai Manzon Allah (SAW) ya umarce su da su zubar da abin da suka tara daga rijiyarsu. Garin kuma su ciyar da taguwarsu, sai ya umurce su da shayar da taguwarsu daga mashayar taguwa.”