Buhari da Muslim | Aminiya

Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

Sa’an nan ta komo Ibrahim (AS) ya tafi sai da ya kai Saniyyah inda ba su ganinsa, sai ya fuskanci Dakin Ka’aba da fuskarsa sa’annan ya yi addu’a da wannan addu’a, ya daukaka hannayensa ya ce: “Ya Ubangijinmu! Lallai ne ni, na zaunar da zuriyata a kwari wanda ba ma’abucin shuka ba, a wurin DakinKa Mai alfarma. Ya Ubangijinmu! Domin su tsayar da Sallah. Sai Ka sanya zukata daga mutane su yi gaggawar begen zuwa gare su, kuma Ka azurta su daga ’ya’yan itace, mai yiwuwa ne suna godewa (K:14:37).” Sai mahaifiyar Isma’il ta ci gaba da shayar da Isma’il (AS), tana sha daga ruwan da ya tara mata. Har sai da ruwan shanta ya kare ta ji kishin ruwa danta kuma ya ji kishin ruwa, sai ta rika duba gare shi na fama da kishi. Na shure-shure sai ta mike ta tafi neman ruwa domin ba ta son ganin haka sai ta iske dutsen Safa da ke kusa da ita ta hau ta tsaya kansa, ta fuskanci kwarin tana duba ko za ta ga wani mutum. Sai ta sauka daga Safa sai da ta kai kwarin nan ta dauke gefen taguwarta sa’an nan tafi da sauri irin na mutum mai matukar kokari har sai da ta ketare kwarin. Sa’annan ta tafi ga dutsen Marwa ta tsaya kansa, ta duba ko za ta ga wani mutum ba ta ga kowa ba. Sai da ta aikata haka sau bakwai.” Dan Abbas ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Saboda haka mutane ke yin Sa’ayi (kewayo) a tsakaninsu (Safa da Marwa).” Lokacin da ta fara hangen dutsen Marwa sai ta rika jin wata murya, sai ta ce shiru! Tana nufin da kanta. Sa’annan ta saurara, sai ta sake jin kamar na farko kuma. Sai ta ce, “Shin ko ka ji idan kana da abin taimako wurinka to ka taimaka. Ana nan haka sai ga mala’ika a wurin Zam-Zam ya haka da duddugensa ko ya ce, “da fiffikensa, har sai da ruwa ya bayyana, ta rika dibarsa tana nuni da hannunta kamar sai ta rika kamfata daga ruwa tana zubawa ga salkunan ruwanta yana kara gangara bayan ta kamfata.” Dan Abbas ya ce: Annabi (SAW) ya ce: “Allah Ya jikan mahaifiyar Isma’il (AS) da a ce ta kyale ko ya ce, da ba ta kamafata ba da rijiyar Zam-Zam ta zamo korama mai gudana. Sai ta sha ta shayar da danta. Mala’ikan nan ya ce mata: “Kada kiji tsoron tozarta, lallai wannan Dakin Allah ne wannan yaro shi da babansa za su gina shi. Kuma lallai Allah ba zai tozarta iyalansa ba. Lokacin Dakin ya daukaka bisa ga kasa da kamar karamin tsauni. Koramai na zuwa masa ta rika dibar dama da hagunarta, ta kasance kamar haka har da wadansu ayarin kabilar Jurhum suka zo wucewa da shi (Isma’il) sun fito daga gefen hanyar Kada’u sai suka sauka a karkashin Makka sai suka ga wani tsuntsu yana kewaya sai suka ce: “Lallai wannan tsuntsu na kewaya ne bisa ga wani ruwan sha, bari mu bi wannan kwari mu duba abin da ke cikinsa. Sai suka aika da ’yan aika biyu ko daya wadanda za su nemo musu ruwa, sai suka iske ruwa, suka koma suka ba su labari game da ruwan. Sai suka zo (Annabi SAW) ya ce: “Mahaifiyar Isma’il ita ce kusa ga ruwan, sai suka ce mata: “Ko za ki yi mana izinin mu yi masauki kusa da ke? Ta ce, “Na’am, amma ba ku da wani hakkin mallakar ruwan nan. Suka ce, “Na’ama.”

Dan Abbas ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Sai mahaifiyar Isma’il ta yarda da su saboda tana son zama da mutane, sai suka yi masauki suka aika zuwa ga iyalansu suka zo suka sauka tare da su, har suka kasance su ne masu gidaje. Yaron nan ya girma ya koyi magana da Larabci daga gare su. Ya fi su kuzari kuma ya ba su sha’awa da ya girma, ya kai shekarun karfi suka aurar masa da wata ’ya daga cikinsu.