Buhari da Muslim | Aminiya

Buhari da Muslim

    Fassarar Salihu Makera

Tare da Sheikh Yunus Is’haq Almashgool, Bauchi

Ana nan haka mahaifiyar Isma’il ta rasu, sai Ibrahim (AS) ya zo domin duba abin da ya bari a bayan Isma’il (AS) ya yi aure bai iske Isma’il ba. Sai ya tambayi matar (Isma’il) game da shi sai ta ce: “Ya fita don ya nemo mana abinci, sa’annan ya tambaye ta game da rayuwarsu da kamannin zamansu. Sai ta ce: Muna cikin sharri, kuma muna cikin kunci da tsanani ta kai kuka gare shi.” Sai ya ce: “Idan mijinki ya komo ki isar masa da sallama, kuma ki ce masa ya musanya madaurin kofarsa.” Lokacin da Isma’il (AS) ya komo kamar ka ce, sai ta hiranta masa wani abu, sai ya ce: “Shin wani mutum ya zo muku? Ta ce, “Na’am, wani tsoho mai kama kaza-da-kaza ya zo ya tambaye mu game da kai na ba shi labari. Ya tambaye mu rayuwarmu, sai na ce masa ina cikin wahala da tsanani.” Sai (Isma’il) ya ce: “Shin ko ya yi miki wata wasiyya da wani abu? Ta ce: “Na’am, ya ce: In yi maka sallama, kuma ya ce, ka musanya madaurin kofarka.” Sai ya ce: “Wannan ai shi ne mahaifina, kuma ya umarce ni da in rabu da ke, to ki tafi zuwa ga iyalanki, ya sake ta.” Sai ya auri wata mace daga cikinsu, Ibrahim (AS) ya zauna bai zo gare su ba gwargwadon yadda Allah Ya so. Sa’annan ya zo bayan haka bai iske shi ba, ya shiga ga matarsa ya tambaye ta game da shi (Isma’il) ta ce: Ya fita neman mana abinci ya ce: “To yaya kuke? Ya tambaye ta game da rayuwarsu da kamannin zamansu sai ta ce: “Muna cikin alheri da yalwata kuma ta yi wa Allah Mai girma da Daukaka yabo. Sai (Ibrahim AS) ya ce: “Mene ne abincinku? Ta ce, “Nama, ya ce, “Mene ne abin shanku? Ta ce, “Ruwan nan.” Sai ya ce: ‘Ya Allah! Ka sanya albarka cikin abincinsu da abin shansu.” Annabi (SAW) ya ce: “Lokacin ba su da hatsi da akwai sai ya rokar musu Allah a kansa. Ya ce: “Don haka (cin nama) ba su zama abinci ga kowa a Makka face ya samu bacin ciki sai da wanda ke zaune cikinta (saboda cin nama da ruwa kadai a rayuwar mutum na da hadari face mutanen Makka).” Sai (Ibrahim AS) ya ce: “Idan mijinki ya komo ki yi masa sallama, kuma ki umarce shi da kara tabbatar (daure) marufin kofarsa. Lokacin da Isma’il (AS) ya komo sai ya ce: “Shin wani mutum ya zo muku? Ta ce, “Na’am, wani tsoho ya zo mana mai kyan kamanni ta yabe shi. Kuma ya tambaya game da kaina ba shi labari cewa ina lafiya ya ce: “Shin ya yi miki wasiyya da wani abu? Ta ce, “Na’am, ya yi maka sallama kuma ya umarce ka da ka tabbatar da marufin kofarka. Ya ce: “Wannan mahaifina ne, kuma ke ce marufin kofa, ya umarce ni da in tabbatar da ke ma’anar in rike ki. Sa’annan (Ibrahim AS) ya zauna ga barinsu bai zo ba gwargwadon abin da Allah Ya so. Sa’annan ya zo a bayan haka ya iske Isma’il (AS) a karkashin itaciya kusa da Zam-Zam. Lokacin da ya gan shi sai ya mike suka wa juna abin da uba ke yi wa dansa, shi ma ya yi abin da da ke yi wa mahaifinsa. Sai ya ce: Ya Isma’il! Lallai Allah Ya umarce ni da wani al’amari, to ka aikata abin da Ubangijinka Ya umArce da shi. Ya ce, “Za ka taimake ni? Ya ce, “Zan taimake ka.” Ya ce: “Lallai Allah Ya umarce da in gina wani daki a nan, sai ya yi nuni bisa tudun nan madaukaki da abin da ke gafensa. A wannan lokacin ya daukaka ginshikin Dakin (Ka’aba). Isma’il ya rika zuwa da duwatsu Ibrahim (AS) yana gini har sai da ginin ya yi bisa. Sai ya zo da dutsen nan ya sanya saboda ya rika tsayuwa kansa na gini Isma’il yana mika masa duwatsu alhali suna cewa: “Ya Ubangijinmu! Ka karba mana lallai ne Kai Mai ji ne Masani.” Ya ce, “Sai suka gina har sai da suka kewaya Dakin suna cewa: “Ya Ubangijinmu! Ka karba mana, lallai ne Kai Mai ji ne Masani.” (K:2:127).