Buhari da Muslim | Aminiya

Buhari da Muslim

    Salihu Maqera

Tare da Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

323. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce, Ukailu ya ba ni labari daga Dan Shihab ya ce, na ji Urwatu ya ce: “A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Sai Annabi (SAW) ya komo zuwa ga Khadija zuciyarsa tana makyarkyata (kadawa), sai ta tafi da shi zuwa ga Waraka dan Nawfal ya kasance mutum ne da ya shiga addinin Nasara a Jahiliyya. Yana karanta Linjila ya fassara da Larabci. Sai Waraka ya ce masa (Annabi) me ka gani? Ya ba shi labarin sai Waraka ya ce: “Wannan ai shi ne Manzon Alheri da Allah Ya aiko shi ga Musa, kuma da dai zan iske ranarka (koyarwarka) da zan taimake ka taimako mai karfi.” Kalmar Namusu tana nufin ma’abucin sirri wanda ke kai shi ga waninsa.”

Babi na Goma Sha Tara:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Shin labarin Musa ya zo maka, lokacin da ya ga wata wuta. Sai ya ce wa iyalinsa, “Ku dakata, lallai ne ni, na tsinkayi wata wuta, tsammani in zo muku da makamashi daga gare ta, ko kuwa in samu wata shiriya a kan wutar. Sa’an nan a lokacin da ya je mata, aka kira shi. Ya Musa! Lallai ne, Ni ne Ubangijinka, sai ka debe (cire) takalma. Lallai ne kana a rafin nan abin tsarkakewa na Duwa.” (K:20:9-12).

Fassarar kalmomi saboda takaitawa mun bar su a tafi wurin malamin wannan fanni ko ka duba littafin Tafsiri (bol.7).

324. An karbo daga Hudbatu dan Khalid ya ce: “Hammamu ya ba mu labari ya ce, Kattada ya ba mu labari daga Anas dan Malik daga Malik dan Sa’asa’a cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ba su labari game da daren da aka tafi da shi. Har sai da ya kai ga sama ta biyar sai ga Haruna (AS), Jibrilu ya ce, “Wannan Haruna ne, ya yi masa sallama ya amsa. Sa’an nan ya ce “Maraba da dan uwan kwarai Annabin kwarai.”

Babi na Ashirin:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Sai wani mutum mummini daga jama’ar Fir’auna wanda ke boye imaninsa ya ce: “Shin za ku kashe mutum domin ya ce: Ubangijina Allah ne alhali ya zo muku da hojjoji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan ya kasance makaryaci ne karyarsa tana kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sashen abin d yake yi muku wa’adi zai same ku. Lallai ne Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai barna mai yawan karya.” (K:40:28).

Babi na Ashirin da Daya:

Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Shin labarin Musa ya zo maka…” (K:79:15). Da fadarSa cewa: “Allah Ya yi magana da Musa kai tsaye (ba tare da shamaki ba)” (K:4:164).

325. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham dan Yusuf ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Zuhuri daga Sa’id dan Musayyab daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: ‘Manzon Allah (SAW) ya ce a game da daren da aka yi tafiya da shi: “Na ga Musa (AS) sai na gan shi mai kamun jiki kamar ka ce shi mutum ne daga kabilar Shanu’ah. Kuma na ga Isa (AS) sai na gan shi madaidaici mai launin ja kamar ya fito daga Dain wanka. Amma kuma ni na fi kama da Ibrahim (AS) a kan ’ya’yansa. Sa’annan aka zo mini da wasu korre biyu cikin dayansu akwai nono, kuma dayan akwai giya. Sai (Jibrilu     AS) ya ce: “Ka sha daga wanda duk ka so. Sai na dauki nono na sha shi. Sai aka ce mini: Ka zabi sunnah, amma lallai kai da ka dauki giya da jama’arka sun yi dagawa (sun bace).”

326. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu’abah ya ba mu labari daga Kattada ya ce, na ji Abu Aliyatu ya ce Dan Baffan Annabinku ya ba mu labari (yana nufin Dan Abbas) daga Annabi (SAW) ya ce: “Bai dace ba ga kowa ya ce, ni na fi Yunus dan Matta alheri, ya jingina shi ga babansa.” Kuma Annabi (SAW) ya amabata game da tafiyar darensa cewa: Musa (AS) mai kamun jiki ne dogo kamar mazan kabilar Shanu’ah. Ya ce: Isah (AS) mutum madaidaici, ya ambaci Malik ne mai tsaron wuta, kuma ya ambaci Dajjal.”

327. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Ayyuba Sikhtiyani ya ba mu labari daga Sa’id dan Jubair daga babansa daga Dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Annabi (SAW) lokacin da ya iso Madina ya iske su suna azumin wani yini wato Ashura (goma ga watan Muharram). Sai suka ce, “Wannan yini ne mai girma, yinin da Allah Ya kubutar da Musa (AS), kuma ya nutsar da Fir’auna a cikin teku. Saboda haka Musa (AS) yake azumtar yinin don godiya ga Allah. Sai (Annabi) ya ce: “Ni ne na fi cancanta da Musa a kansu, sai ya azumci wannan yini. Ya umurta da yin azuminsa.”