✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Osinbajo sun sa wa Janar Farouk anini

Buhari da Osinbajo sun lika masa aninin ne a safiyar Laraba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Babban Hafsan Sojan Kasan Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya, kwalliyar anini a safiyar Laraba.

Buhari tare da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun lika masa aninin ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan kammala kwalliyar ce kuma Shugaba Buhari ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa wanda aka saba gudanarwa duk Laraba.

Kwalliyar anini ta mukamin Babban Hafsan Soja da aka yi wa Janar Farouk a Fadar Shugaban Kasa
Buhari lokacin da yake sa wa Janar Farouk hula
Manjo Janar Farouk Yahaya a Fadar Shugaban Kasa
Manjo Janar Farouk Yahaya tare da iyalinsa da Hafsan Hafsoshin Soji Janar Lucky Irabor da IGP Usman Alkali Baba

Tun a watan Mayun da ya gabata ne Buhari ya nada Janar Farouk a matsayin jagoran rundunar sojan kasa.

Hakan na zuwa ne bayan ’yan kwanaki da rasuwa wanda ya gada, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru, ya rasu a wani hatsarin jirgin sama a Jihar Kaduna.